Wani masani a harkar kiwon lafiyar dan Adam, Olu Aijota, ya bayyana ababen da suka dace mutum mai azumi ya rika ci a wannan wata mai tsarki.

Ga dai kadan daga ciki kamar yadda muka tsakuro daga shafin Premium Times;


Yana da kyau a fara karya azumi da shan ruwa sai dai kuma ba a son a rika kwankwadar ruwa a lokaci guda wanda hakan yana iya sa ciki ya daure.


Cin Ganye Da Abinci Mai Gina Jikin Dan Adam
Ya fi dacewa mai azumi ya nemi ganye ko kayan marmari yayin buda baki. Irin abin da ake nufi sun hada da kifi, lemu, gwaiba, abarba, ayaba, ganye da sauran su

A Guji Sukari

Dole mai azumi ya guji abubuwa irin su sukari da ice cream ko sinadarin soda. Irin wadannan sinadarai na kara nauyi don haka dole a guje su a cikin watan Ramadan.

A takaice dai ba a son cin abinci mai nauyi yayin azumi kuma ana bukatar a rika motsa jikin kafin ayi buda baki wannan zai kara lafiya.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top