Wata sanarwa da malaman suka sanya wa hannun ta bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne saboda ayyukan da suke gabansu.
Sai dai a tattaunawar da BBC ta yi da shi ta waya, Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce sun fita daga gwannatin ne saboda sun ga ba a bukatar aikinsu.
Shi kuwa a cikin takardar da ya mika ta murabus dinsa Shaikh Abba Adam Koki ya ce ya ajiye aikin ne saboda dalilan rashin lafiya.
Shaikh Daurawa dai shi ne babban kwamandan Hisbah ta jihar Kano, shi kuma Shaikh Abba Koki shi ne shugaban hukumar alhazai ta jihar.
Malam Nazifi Inuwa ya rike mukamin kwamishina na biyu a hukumar Zakka ta jihar Kano, yayin da shi kuma Malam Abubakar Kandahar ya rike mukamin kwamishinan shari'a na daya na jihar ta Kano.
Dangantaka tsakanin gwamnan na Ganduje da wasu daga cikin malaman ta jima da yin da tsami, inda ake zaune ta ciki-na-ciki.
Murabus din malaman na zuwa ne kasa da mako daya bayan gwmanan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa akwai wasu bara-gurbi a hukumar Hisbah.
Yayin da yake jawabi a wajen taron auren zawarawa da aka gudanar a makon farko na wajen Mayu, gwamnan ya ce ana muna-muna da cuwa-cuwa a hukumar Hisbah, abin da ya ce dole ne a tsaftace hukumar.
Dangantakar ta kara yin tsami ana daf da zaben gwamna, bayan da wani bidiyo da aka watsa ta kafofin sada zumunta ya nuna wasu malaman da ke rike da mukamin gwamnati sun kai ziyarar goyon baya ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar PDP.
Kwankwaso shi ne babban abokin hamayyar gwamna Ganduje, duk da cewa ba shi ya nemi takarar gwamnan ba.
Mafi yawan malaman da suka ajiye aikin dai tsohon gwamna Kwankwaso ne ya nada su a mukaman, yayin da shi kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ci gaba da aiki da su bayan ya zama gwamna a 2015.
Rahoto : BBChausa.
©HausaLoaded
Post a Comment