A ranar Asabar 5 ga watan Mayun 2019 ne gwamnatin Kano ta aurar da zawarawa 3000 a fadin jihar.

Gwamnatin jihar ta ce ta biya kusan miliyan 30 a matsayin sadakin ma'auratan.

An gudanar da daurin auren ne a duka kananan hukumomin Kano 44.

Gwamna Abdullahi Ganduje shine waliyan angwayen shi kuma Sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu shine waliyyan amaren da aka daurawa aure wanda adadin su ya kai 3000- maza 1500 mata 1500 kenan.



Post a Comment

 
Top