A yanzu dinnan mun samu rahoton cewa, Sarakin Musulmi Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ya bayar da umurnin a yi shellar bayyanar sabon jaririn watan Azumin Ramalana cikin wasu sassan kasar nan.

Hukumar kwamitin kula da laluben wata ta kasa, NSCIA, National Moon Sighting Committee, ita ce ta bayar da wannan sanarwa ta gaggawa a shafin ta na zauren sada zumunta na Facebook.

Hukumar ta bayar da shaidar cewa, sanarwar na zuwa ne bisa ga umurnin Mai Martaba Sarkin Musulmi, wanda ya nem a shellatawa a al'umma wannan rahoto na maraba da watan Azumin na shekarar 1445 bayan hijirar fiyayyen halitta Manzon tsira daga birnin Makka zuwa Madina.

Sanarwa kamar yadda hukumar NSCIA ta bayyana, a halin yanzu ana ci gaba da tattara sakonni dangane da bayyanar sabon jaririn watan Azumin Ramalana a wasu daban-daban cikin fadin kasar nan.


A yayin da ake ci gaba da tattara sakonni da rahotanni dangane da bayyanar sabon watan, Sultan ya nem daukacin al'ummar Musulm da ke fadin Najeriya a kan daura damarar tare da kudirtar niyya ta gudanar da azumi kamar yadda addinin Islama ya shar'anta.

Kasancewar ta sunna mai karfin gaske, Sultan na Sakkawato ya yi kira na neman a fara gudanar da sallolin tarawi domin samun duk wani tabarraki da kwankwadar romon rahama da ya ke tattare da shi.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top