Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya ya bayyana shugabannin arewa da malamai a matsayin munafukai

- Tsohon Sanatan yayi wannan maganar ne bayan gwamnati ta bayyana kungiyar 'yan Shi'a a matsayin 'yan ta'adda

- Ya ce idan har magana ce ta 'yan Shi'a zaka ji manyan arewa na saka baki amma idan Boko Haram ne zaka ji su sunyi tsit

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani yayi magana kan shugabannin arewa akan goyon bayan da suka nuna wajen bayyana kungiyar 'yan uwa Musulmai wacce aka fi sani da Shi'a a matsayin 'yan ta'adda.

Idan ba a manta ba dai an bayyana kungiyar 'yan shi'an a matsayin 'yan ta'adda bayan wani rikici da suka yi da jami'an 'yan sanda a babban birnin tarayya Abuja.

Kungiyar dai ta riga ta saba gabatar da zanga-zanga a kowanne sati inda take neman gwamnati ta saki shugabansu, Malam Ibrahim El-Zakzaky. A cikin zanga-zangar da suka yi ne cikin wani mako da ya gabata har tayi sanadiyyar mutuwar wani ma'aikacin gidan talabijin na Channels.



Bayan haka kuma wannan zanga-zanga da suka yi ta jawo sanadiyyar mutuwar mutuwar wani babban jami'in dan sanda da kuma wani dan bautar kasa.

Wannan lamari da ya faru dai ya jawowa kungiyar bakin jini a sassa daban-daban na kasar nan. Da yake mayar daa martani akan hakan Shehu Sani ya bayyana shugabannin arewa a matsayin munafukai da suka goyi bayan batawa kungiyar suna.

Ga abinda ya ce: "Manyan 'yan siyasa na arewa da Malamai sun fi dukan kirji su fito suyi magana idan aka ce lamari ne na 'yan Shi'a, amma kuma sai kaji su tsit idan aka ce magana ce ta Boko Haram."

® Legit

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top