Kakakin majalisar dokokin jihar Kano Kabiru Alhassan Rurum, ya ce sabuwar dokar da suka gabatar ta bai wa shugaban majalisa da mataimakinsa fansho na har abada za ta taimaka wajen ragewa 'yan siyasa da suka sauka daga mukamansu radadin wahala.

Majalisar dokokin jihar ta gabatar da sabon kudurin dokar ne a ranar Talata, wanda zai bai wa kakakin majalisar da mataimakinsa fansho tsawon rayuwarsu da kuma zuwa kasashen waje duba lafiyarsu duk shekara.

Rurum ya shaida wa BBC cewa an yi sabuwar dokar ne "don a rage cin hanci da rashawa da kuma hana 'yan siyasa shan wahala a yayin da ba sa kan mukamai."

Wannan doka dai na shan suka sosai ganin yadda talauci ya yi wa mutanen kasar katutu. Kuma ita ce doka ta biyu da majalisar ta gabatar a wannan makon da suka jawo ce-ce-ku-ce.

Baya ga ba su fansho na har abada, sabuwar dokar za kuma ta ba su damar mallakar sabbin motoci duk bayan shekara hudu.

Sannan za su samu damar zuwa kasashen waje domin duba lafiyarsu, ko kuma duk asibitin da ya yi musu a fadin Najeriya tsawon rayuwarsu.

Sai dai ba a san adadin yawan kudin fanshon da za su dinga karba ba, amma idan har gwamnan jihar ya amince da dokar, to Kano za ta zamo jiha ta farko da za ta fara amfani da irin wannan dokar.

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da ke fama da matsanancin talauci a duniya, kuma Kano ce jihar da ta fi yawan al'umma.
BBChausa.

Post a Comment

 
Top