Wasu rahotanni na nuna cewa gwamnatin jihar Kano na yunkurin sauke sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II daga sarautarshi. Wannan na zuwane bayan da hukumar yaki da rashawa ta jihar ta tono wani tsohon laifi da ake tuhumar masarautar Kanon inda zata ci gaba da bincike.

The Cable ta ruwaito cewa, binciken akan yanda aka kashe wasu kudi ne na masarautar Kanon da sukakai biliyan 6 ba tare da amincewar gwamnatin jiha ba karkashin mulkin Sarki sanusi. An fara bincike kan wadannan kudi ne jim kadan bayan da Sarki Sanusi yayi magana akan kwangilar da gwamnatin jihar Kano ta baiwa kamfanonin kasar China da kuma tafiye-tafiyen gwamna Ganduje a shekarar 2017 amma daga baya an tsayar da binciken.

Yanzu shine aka sake tadoshi, kamar yanda The Cable ta ruwaito. A wata takardar sammace dake dauke da ranar 2 ga watan Mayu 2019, hukumar hana rashawa ta Kano ta aikewa wani Isa Bayero da ya gurfana gabanta dan yayi bayanin yanda aka kashe kudi daga shekarar 2013 zuwa 2017 a masarautar Kano a wasu rasidan dake dauke da sunanshi.

Sauran wadanda za'a tuhuma akwai Muhammad Sanusi Kwaru wanda shine akawun masarautar, da Mannir Sanusi, wanda shine shugaban ma'aikata da kuma Danburam Mujittaba da Falakin Kano.

Hakanan a ranar Litinin din data gabata, kakakin majalisar jihar, Kabiru Alhassan Rurum ya karanto wata wasika daga wani Ibrahim Salisu da wasu sauran mutane dake bukatar a kirkiro karin masarautu a yankunan Karaye, Bichi, Rano da Gaya na jihar ta Kano.

Wani ma'aikacin gwamnatin jihar ta Kano da baiso a bayyana sunanshi ya gayawa The Cable cewa, Gwamnan Kano naso ya cire sarkin Kano idan kuma hakan bata samu ba to zai yi kokarin kirkirar masarautun da zasu ragewa sarki Sanusi karfi.

Post a Comment

 
Top