Abubuwa guda 20 da basa karya Azumi:

1-Kwana da janaba a jiki.Annabi ya kan wayi gari da janaba kuma yana mai azumi.
@Bukhari

2-Kurkure baki da shaqa ruwa.

3-Sanya tozali da rana.
@Fathul Bari

4-Sanya maganin ciwon ido.

5-Sanya maganin ciwon kunne.

6-Fitar maniyyi ta mafarki da rana.
@Subulussalam

7-Yin qaho.
@Bukhari

8-Rungumar mace da sumbatarta in ba ka da kaifin sha’awa.

9-Zuba ruwa mai sanyi a fuska ko a kai.

10-Dandana abinci amma a tofar bayan
Dandanawar.

11-Amai ba da gangan ba.

12-Maganin da masu cutar ‘ASMA’ ke anfani da shi wato( Inhaler) lokacin azumi ba ya karya azumi.

13-Shaqa maganin mura.

14-Dibar jini a jikin mai azumi ba ya karya azumi.
@Fatawas-siyam, Uthaymin

15-Cin abinci da mantuwa. [Allah ne ya ciyar da kai babu komi azuminka na nan].

16-Yin asuwaki ko makilin da burushi.
@Siyamu ramadan na Jamil Zainu.

17-Yin wanka a rafi

18-Zuba ruwa a kai domin jin sanyi.

19-Yin allura a jiki da sunan Magani bata
karya azumi.

20-Cire haqori ko cikesa ba ya karya azumi.
@Munajjid 70 question on Fasting.



Idan mace tana da ciki sai ta ga jini ya zubo mata a gabanta, babu komai domin wannan ba
jinin haila ba ne, azuminta yana nan bai lalace ba,ciwo ne ta nemi magani.Amma da a ce tana haila sai ta ga hailarta ta dauke bayan alfijir ya fito ba zata yi azumi ba.
@Fatawa siyam Usaimin.
Allah ne mafi sani.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top