Ina masu neman rage kiba? ku huta da sayen magunguna ko shayin da ba ku san wasu sunadarai aka yi amfani da su ba waje hada su, ga wani hanya nan mafi sauki wajen rage kiba wanda za ku iya hada da kanku ba sai kun je ku siye ba.
ABUBUWAN DA AKE BUKATA
1. Ginger
2. Garlic
3. Lemon
4. Tea da kike using
5. Carrots
Yadda Ake Hadawa : Ki fere lemon ki yayyanka, haka nan garlic ki cire bawon ki dan yanka su. Ki wanke lemon ki yanka shi tare da bawon shi, haka nan ma carrots.
Sai ki zuba ruwa a tukunya ki juye su, zaki iya matse
juice din lemon before ki saka shi a ciki. In suka dahu sai ki tace ki rinka sha da dumin sa safe da yamma. Ba dole sai kin cika kofi ba dan dai dai mai 100ml ma ya isa. Sai ki dan jijjaga jinin jikinki kadan wato ki dan yi tsalle ki yi zufa shikenan.
Baya barin fat ya zauna a jiki sai na ba a rasa ba, yana sanya Tommy ya zama flat. In dai kina sha a kai baki tsallake to komai zaki iya ci kuma ba zaki rinka yin kiba ba. In kina son ganin yayi miki abun da kike so cikin yan watanni ki rinka haďa wa da Apple cider venegar (ruwan khal).
Carrots in kin sanya shi yana kashe kamshin tafarnuwa ne ga wanda baya so. Sannan tea zaki iya saka Green tea ma in kin so tun da shima yana taimaka wurin rage fat.
Irin wadannan shayin ba ragewar yau ko gobe bane. In ka dage sha ya bi jikinka ne sosai zai fara maka aiki. Ba ka sha yau sai kuma bayan sati ba.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment