Masana sun gudanar da bincike kan yadda aka yi ‘Furfura’ wato farin gashi ke fitowa wasu mutane wanda ke da karancin shekaru inda a da tsofaffi ne ake dangantawa da furfura.

Binciken na masanan ya bayyana cewa ba duka Furfura bace take ke dangantaka da tsufa ko kuma ke zama halitta daga Allah, akwai dalilai da dama da ke sa bayyanar Furfura a jikin dan Adam.


Sun ce fitowar Furfura a jiki ya rabu kashi biyu ne, akwai wanda nasu halitta ce daga Allah, akwai kuma wanda ke fitowa sakamakon rashin garkuwar jiki mai karfi.

Sun kara cewa, an halici jikin mutum da garkuwa da suke taimakawa wurin kare mutum daga kamuwa da cututtuka. Furfura kan fito a jikin mutum musamman yaro karami idan garkuwar jiki nasa bashi da karfin kare shi daga kamuwa da cututtuka.”

Domin guje wa irin haka masanan sun bayyana wasu hanyoyin da za su taimaka wa mutum wajen gujewa samun garkuwar jiki mara karfi.


1. Yawaita cin abincin dake dauke da sinadarin dake karfafa garkuwar jiki kamar su ganye, kayan lambu, madara, kifi, da sauransu.

2. Samun Isasshiyar hutu musamman ga wadanda suke ganin cewa hutawa lalaci ne.

3. Rage damuwa domin yawan damuwa na kawo tsufa da wuri.

4. A dunga motsa jiki domin yana taimakawa wurin bunkasa garkuwar jiki.

5. A rage cin abincin kamar shan giya, yawan cin maiko, kanzon tukunya da makamantan su.

6. A dunga tsaftace jiki, muhalli da abinci.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top