Shin Baik
Daga Sheikh Abdulwahhab Abdullah
Mas’alolin Aure Fitowa Ta 18 (Mene Ne Hukuncin Auren Dole A Musulunci? Shin Baiko Aure Ne?)
Bayani ya gabata akan nau’ikan aure da dama wadanda shari’a ta hana.

TAMBAYA:
Mene ne hukuncin auren dole a Musulunci?
AMSA:

Babu auren dole a Musulunci bisa dalilai mafiya inganci na maganar malamai. Sai dai wadansu malamai kamar Imam Malik da Imamus Shafi’i da Ishak Ibn Rahawaihi da daya daga cikin fadin Imamu Ahmad sun tafi a kan cewa uba zai iya aurar da `yarsa ko da kuwa ba ta so, sun karfafi maganarsu da hujjoji kamar haka; 1- An rawaito hadisi daga Urwatu Ibn Zubair daga babansa daga Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta ce:
Ma’ana: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya aure ni ina da shekara shida, kuma ya tare da ni ina `yar shekara tara..
Imamus Shafi’i (Allah ya ji kansa) ya ce:
Ma’ana: Hakika Sayyadina Aliyu radhiyallahu anhu ya aurawa Sayyadina Umar radhiyallahu anhu `yarsa Ummu Kulsum ba tare da izininta ba..
Kamar yadda aka rawaito a cikin hadisin Hasan Ibn Hasan daga babansa cewa:
Ma’ana: Sayyadina Umar radhiyallahu anhu ya nemi auren Ummu Kulsum a wurin Sayyadina Ali radhiyallahu anhu, sai Sayyadina Ali radhiyallahu anhu ya ce masa: ai ta yi kankanta, sai Sayyadina Umar radhiyallahu anhu ya ce: na ji Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce: “Dukkan wani sababi da nasaba abin yankewa ne ranar Alkiyama, sai dai sababina da nasabata”, don haka nake son na hada nasabata da ta Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama , sai Sayyadina Ali radhiyallahu anhu ya cewa Sayyadina Hasan da Sayyadina Husain ku aura wa amminku (ita), sai suka ce: ai ita mace ce daga cikin mataye tana da zabin kanta, sai Sayyadina Ali radhiyallahu anhu ya tashi cikin fushi ya kama tufafin Sayyadina Hasan radhiyallahu anhu, sai Sayyadina Hasan radhiyallahu anhu ya ce: ba zan iya jurewa da fushinka ba ya babana (mun yarda da abin da ka fada), daga nan sai suka aura masa ita..
Imamus Shafi’i (Allah ya ji kansa) ya ce:
Ma’ana:
Zubair Ibn Auwam radhiyallahu anhu ya aurar da `yarsa alhali tana `yar karama. Haka kuma mutane da yawa daga cikin Sahabban Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama sun aurar da `ya`yansu alhali suna kanana. Sannan ya ci gaba da cewa: da aurar da budurwa bai halatta ba sai da izininta, da ba za a aurar da ita ba sai da yardarta..
Haka kuma Imamus Shafi’i (Allah ya ji kansa) ya fassara cewa:
Ma’ana: Neman shawararta kan zama dadada rai ne..
Sannan ya ci gaba da cewa: an rawaito hadisi daga Abdullahi Ibn Umar radhiyallahu anhu ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce: ﻭﺍﻣﺮﻭﺍ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻲ ﺑﻨﺎﺗﻬﻦ Ma’ana: Ku nemi shawarar iyaye mata dangane da `ya`yansu mata..
Kuma ya ce:
Ma’ana: Babu wanda yake da sabani a kan cewa iyaye mata ba su da wani iko sai dai ma’anarsa dadada rai ake nufi..
Haka kuma an rawaito daga Imam Ibrahimun Nakha’i ya ce:

Ma’ana: Uba zai iya tilastawa `yarsa budurwa..

Imamus Sha’abi ya ce: ﻻ ﻳﺠﺒﺮ ﺍﻻ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪ Ma’ana: Babu wanda zai iya tilastawa budurwa sai uba..

Haka kuma sun kara kafa hujja da fadin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama cewa: ﻻ ﺗﻨﻜﺢ ﺍﻟﻴﺘﻴﻤﺔ ﺇﻻ ﺑﺈﺫﻧﻬﺎ Ma’ana: Ba a aurar da marainiya sai da izininta..

Sai suka ce: wannan hadisin ya nuna cewa, idan budurwa ce, za a iya aurar da ita ba tare da izininta ba..
Sai dai duk da wadannan dalilai da suka kawo, Imamu Malik da Imamus Shafi’i da Imam Ibn Abi Laila sun ce: Matukar akwai cutarwa bayyananniya a cikin auren dole, to, uba ba shi da ikon ya aurar da `yarsa karama ko babba. Wannan shine fadin Imamu Ahmad da Imam Ishaq da ma’abota ilimi masu yawa..

Magana ta biyu ita ce malaman da suka ce auren dole bai halatta ba, sun karfafi maganarsu da hujjoji kamar haka; Hadisi ya tabbata daga Abu Huraira radhiyallahu anhu ya ce: Hakika Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce:

Ma’ana: Ba a aurar da bazawara sai an nemi izininta da yardarta. Kuma ba a aurar da budurwa sai da yardarta. Sai Sahabbai suka ce: Ya Rasulallahi sallallahu alaihi wa sallama yaya yardarta za ta kasance? Sai ya ce: Shirunta (shi ne yardarta)..

Babban malaminnan Ibn Athir ya ce: fadin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama game da bazawara cewa: “A nemi izininta da yardarta”. Hakan yana nufin al`amarinta yana hannunta, sai ta yarda kuma ta furta amincewarta..

Haka kuma neman yardar budurwa ya zama dole, amma shirunta shi ne izininta..

Haka kuma Imamut Tirmizi ya ce: Maganar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama cewa a nemi izini da yarda daga bazawara yana nuna cewa tana da hakki a sha`anin auren ta fiye da waliyyinta. Wannan kuma shi ne ra`ayin mafi yawan malamai..

Saboda haka waliyyinta ba zai aurar da ita ba, sai da yardarta tare da amincewarta. Idan kuma ya aurar da ita ba tare da izininta ba, to, wannan auren batacce ne bai inganta ba. Sannan ya kara da cewa mafi yawan malamai a cikin su akwai malaman Kufa da sauransu sun ce: Idan uba ya aurar da budurwa bayan ta balaga ba tare da izininta ba, kuma ba ta yarda da auren ba, to, shi ma wannan auren batacce ne bai inganta ba..
Haka ne ya sanya Imamul Bukhari ya bude babi da fadin cewa: “Idan mutum ya aurar da `yarsa alhali ba ta so, to, auren abin mayarwa ne (ma’ana auren bai dauru ba)”..

Sannan sai kuma ya kawo hadisin Khansa’u Bint Khizam
Ma’ana:

Hakika babanta ya aurar da ita alhali tana bazawara, sai ba ta so auren ba, sai ta je ta fadawa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama , sai ya rushe auren..
Amma a ruwayar Imamus Sauri ya nuna cewa: Khansa’u ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ , budurwa ce ba bazawara ba ce..

Haka kuma Imam Abu Dawud ya rawaito daga Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu anhu cewa:

Ma’ana: Hakika wata yarinya budurwa ta zo wurin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama , sai ta ambata masa cewa: babanta ya aurar da ita alhali ba ta so, sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ba ta zabi..

Wadannan ruwayoyin sun tabbatar da cewa: idan aka aurar da budurwa ba tare da yardarta ba, to, auren bai dauru ba, rusasshe ne har abada..

Dangane da aurar da karamar yarinyar da ba ta balaga ba kuwa sun ce: uba zai iya aurar da ita ba tare da neman izininta ba, matukar auren zai zamar mata maslaha nan gaba, kuma ita kanta za ta yi lale da wannan auren bayan ta yi hankali, kamar yadda Imam Ibn Munzir ya fada cewa: Ma’abota ilimi sun hadu a kan cewa, uba yana da ikon ya aurar da `yarsa karama idan har wannan mijin da za a aurawa, ya dace da ita ta fuskar matsayi, wannan kuwa ko da ba ta sonsa..

Sai dai Ibnu Hazmin ya ki amincewa da wannan magana inda ya ce: Uba ba shi da ikon aurar da yarinya karama, har sai ta balaga kuma ya nemi yardarta..

Daga wadannan bayanai da suka gabata za mu fahimci cewa, bai halatta ba uba ya aurar da `yarsa ko bazawara ko marainiya da ke karkashinsa sai da yardarta. Amma uba zai iya aurar da yarinya in har ya samar mata miji mai matsayin da ba kowa yake samu ba matukar ba ta nuna cewa tana kin sa ba. A nan uba zai iya aurar da ita don moriyar da `yar za ta samu duniya da lahira game da wannan mijin kamar yadda Sayyadina Abubakar radhiyallahu anhu ya aurar da Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama alhalin tana karama. Kuma ma wannan auren na Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ishara ce daga Allah subhanahu wa ta’ala, domin an nunawa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ita a mafarki cewa ga matarka, wanda kuma mun sani cewa mafarkin Annabawa wahayi ne..

Don haka ba dalilin da zai sa mutum ya aurar da `yarsa karama ga wanda ba ta so komai dukiyarsa, domin ba a kiyasin auren Nana Aisha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ da sauran mata, domin ita Allah subhanahu wa ta’ala ne ya zabe ta kuma ya ba ta wannan matsayi..

Kuma mafi yawan auren dole, shi yake kawo mutuwar auren mata wanda yakan sa su fada ayyukan fasadi da karuwanci da sauran abubuwan da ba sa haifar da alheri. Don haka muna nasiha ga iyaye da su tabbata sun tarbiyantar da `ya`yansu bisa tarbiyya ta gari, a kuma zabar musu mazaje na gari. Sannan a yi ta yi musu addu`a wadda za ta amfane su duniya da lahira, saboda addininmu ya bayyana komai na alherin duniya da lahira. Domin rayuwar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama da sahabbansa, darasi ce a gare mu, wanda idan mun rike su, za mu huta duniya da lahira. 

Kuma yana da kyau mu sani cewa, idan mun riki addininmu, sau da kafa, da`awar da Turawan yamma suke yi da sunan ci gaba ko neman `yancin mata ko wayewar kai ta banza, ba za ta cutar da mu ba, domin mu ne a gaba da su. Allah ya sa mu dace amin..


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top