Daga Sadik Tukur Gwarzo
Kashi Na Biyu:
Bayan kwamandan Berber na Andaluz, Tarik ibn Ziyad da hadin gwiwar Gwamnan Afirka Musa Ibn Nusair sun ci gagarumin yaki a daular Iberiya ta Sifen, kuma sun sanya wa wurin suna Andaluz, sai aka bai wa wani kwamanda a rundunar Umayyawa gwamnan kordoba, garin da suka maishe shi babban birnin masarautar Andaluz, aka dora dan Gwamna Musa Abdul’aziz Ibn Musa ibn Nusayr gwamnan Sabilla, wani babban birni da ke masarautar, aka dora shugabanni a sauran garuruwan da aka kwace kuma, sai suka juya suka nufi Damascus domin sanar da Shugaban Musulunci halin da ake ciki.
Wannan fa wani yunkuri ne na daular Umayyad na fadada girmanta gami da cusa Musulunci a sassan duniya. Tunda a shekarar 712 ma, wani babban kwamandan yaki na daular Umayyad din mai suna Muhammad bn kasim ya tafi da dakaru saman Tekun Fasha, inda suka yi yaki har suka kwace yankin Sidh da na Punjab da ke Hindu, sannan suka rinka yake-yake da sarakunan Arewaci da Kudancin Hindu, watau Sarki
Nagabhata na masarautar Chalukya, da Sarki bikramadutya na biyu na masarautar Gurjara Pratihara, wadanda a karshe ba su samu nasarar kwace daulolin biyu ba. Don haka a lokacin da Musa da Tarif suka dawo, sai Khalifan Damaskus ya yi kishin abin da Musa ya yi ba tare da izininsa ba, shi ne ya sa aka daure Gwamna Musa a kurkuku, Tarik kuma ya bar garin tare da yin ritaya. A shekara ta 716 kuma sai Gwamnan Damaskus din dai ya tura aka kashe Gwamna Abdul’aziz dan Musa ibn Nusayr a Sabilla, yana masallaci. Daga nan kuma ya zamo daular kacokan ta zamo a hannun
Masarautar Damaskus, ita ke dora gwamna, ita ce kuma ke saukewa.
A wajajen shekara ta 745 kuma, wata kabilar Larabawa ta bijiro daga tsatson Okba Ibn Nafi Al-fihri, wadda ake wa lakabi da Fihriyawa, wadda kuma ta kwace shugabancin Afirka da na kordoba, wadanda ke karkashin daular Umayyad. Wani mai suna Abdurrahman Ibn Habib al-fihir shi ne ya zamo gwamnan Kairawani ta Afirka (inda Musa ibn Nusayr yake mulki a baya), sai kuma Yusuf Al-fihiri wanda ya zamo gwamnan Andaluz. Don haka a shekarar 748 lokacin da Abbasiyawa suka kwace mulki, sai Fihriyawa suka tura wa Abbasiyya sakon mubaya’a tare da son tafiya tare, amma sai Sarkin Abbasiyawa ya ce sam ba za a yi haka ba, dole sarakunan su sauka
shiku ma ya nada nasa. Wannan ya sa Fihriyawa suka ayyana yaki tsakaninsu da Abbasiyawa, har kuma suka yi shelar cewa dukkan wani Ba’ummiye (Bakuraishen Umayyun) da ya shiga wadannan masarautun zai samu mafaka.
Kodayake, an ce daga baya sarakunan sun canza shawara, saboda suna tunanin idan jinin Umayyawa suka yi yawa a kasarsu, saboda farin jininsu ga al’umma, za su iya tada bore har su kwace mulki daga hannunsu. A wannan shekara ta 748 ne jinsin Abbasiyawa suka karbe mulkin daular Musulunci da Umayyawa ke mulka a Damascus wanda ta samo asali daga Sahabi Mu’awiyya (R.A), Bakuraishe jinin Annabi (S.A.W). Abbasiyawa sun fara mulkinsu a nan Damskus din kafin daga baya su dauke daular daga Damaskus din su maishe ta Baghdad. (Wannan rigima fa dadaddiya ce, warware ta ba abu ne mai sauki ba, amma dai ita ce ta samo asali tun daga asalin Shi’atu Ali, har zuwa Kharijawa, har kuwa Abbasiyawa kuma).
Sai dai akwai Yariman daular Umayyad mai suna Abdurrahman, wanda yake da ne ga tsohon sarkin daular Umayyad ta Damaskus mai suna Mu’awiyya ibn Hisham. Kuma ana masa zaton hawan mulki idan Al-walid ya mutu, saboda an ce tun yana yaro ake ganin alamomin sarauta a jikinsa. Don haka yadda Abbasiyawa suka karbe mulki kuma suke karkashe Umayyawa, ga labari ya zo masa kuma cewa sarkin Abbasiyawa Al-mansur ya tura dakaru don a kawo masa kawunan Umayyawa, hakan yasa ya sulale daga garin Damaskus, a tare da shi akwai dansa Sulaiman dan shekaru hudu, da kaninsa Yusuf da (kannensa) ‘yan uwansa mata, da kuma wani yaronsa Baturen Girka mai suna Bedr.
An ce sun sauka ne a tekun Yufret, suka shiga wani kauye suka buya. Daga bisani dakarun Abbasiyawa masu neman su suka ji labari, suka iso kauyen don su kashe su, amma aka yi sa’a Abdurrahman da Bedr da Yusuf suka tsere, suka bar dansa da ‘yan uwansa mata a kauyen. Suka bi ta wani kauye, dakarun na biye da su har ya zuwa bakin teku. Daganan sai kawai suka shiga tekun Yufret din suna bundun-bundun don su samu damar tsallakewa zuwa gaba, yayin da dakarun ke tsaye a gefe suna musu lallamin cewa su fito babu abin da zai same su. An ce Yusuf ya fara iyo amma ya gaji, sai ya ji tsoron zai nutse, don haka ya koma baya wurin dakarun Abbasiyawa, yayin
da Abdurrhaman ke kiransa da kada ya ji maganarsu, kamar yadda wani masanin tarihi Ahmed Muhammad Al Mokkari ya ruwaito cewa, Abdurrahman yana cewa Yusif “dan’uwana, ka zo gare ni. Ya kai dan’uwana, ka zo gare ni”.
Amma ina, bakin alkalami ya bushe, sai da ya isa gare su. Yana zuwa gare su kuwa sai suka kama shi, suka datse wuyansa tare da jefar da gangar jikinsa a nan, suka tafi da kan don nuna wa sarkinsu. Abdurrahman da Bedar sun tsira amma fa da kyar. Domin kuwa, an ruwaito Abdurrahman din yana bada labari a lokacin da ya zamo sarkin daular Anduluz Bakuraishe na farko yana cewa bai taba tsammanin zai tsira ba, domin bayan sun tsallake gabar teku suna iyo, sai da suka yi gudu kamar ransu zai fita. Abdurrahman da Bedar suka ci gaba da tafiya bayan sun tsallake Tekun Yufrat. Suka shiga ta Falasdinu, suka shige Sinai da egypt, suka shiga kasar Tunisiya suna ta kokarin isa Kairawani, tun da mahaifiyarsa Berber ce kuma ‘yar garin ce, kuma ya ji labarin Sarki Abdurrahaman Al-fihiri ya ce zai bai wa Umayyawa mafaka, bai ji labarin sarkin ya sauya shawara ba.
Bayan wani lokaci suka isa wani gari mai suna Kabili, wanda yake kusa da Kairawani. A nan ne kwamandan sojojin Berber ya sauke su a cikin dakarunsa, sai dai kuma labari yana isa ga Sarki Abdurman Al-fihri na Kairawani cewa Yarima Abdurrahman ya sauka a cikin sojojinsa da ke Kabili, sai nan da nan ya aiko cewa a yi gaggawar kama masa Abdurrahman a kai masa shi.
An ce da daddare matar kwamandan mai suna Tekfah ta taimaka musu, inda suka yi shigar mata suka gudu ba tare da kowa ya sani ba. Don haka, daga wannan tsirar tasu, sai suka yi Yamma. Abdurrahman ya ce babu inda za su nufa sai Andalus, komai zai faru gara ya faru.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment