Mata mu kan fada cikin yanayi na yaudara cikin sauri ba tare da mun farga ba. Musamman idan namiji ya zo da batun auren ki zan yi, mu kan mika duk wata ragamar rayuwar mu a gare shi, muna masu amanna da mika wuya dari bisa dari.
Sam bama hangen da mi yazo a lokacin, mi yasa mu ke sonsa, a'a mu dai babban burin ai ya cika tunda yace aure ne a gaban sa. Amma mi? Shiru shiru yaki ya turo iyayensa a maganar dattijai. Idan kin yi magana kullum sai dai yace miki lokaci yake jira, ko kuwa akwai wani abu da yake son ya kammala, shiru an dau watanni har ya haura shekara babu wani batun shigowar manya a lamarin soyayyar ku.
Shi fa namiji matukar yana son abu to yana iya yin komai dan ganin ya mallake shi, koda kuwa mazaje dubu ke sonki babban burin shi a ce shi ne yayi zarra. Zai yi duk wani abu dan ganin ya mallake ki, kin zama ta shi. Amma matukar kuka shafe shekara ko watanni babu wani batun shigowar manya a lamarinku to ki tabbata ba auren ki ya zo yi ba, ko kuwa ya zo da nufin aurenki amma cikin dan zaman da kuka yi wasu dalilai ya say a kasa yanke shawara akan ki.
Akwai dalilai da dama da zan kawo wadanda zasu haska miki hanya ki tabbatar da cewa kodai ba aurenki ya zo yi ba, ya zo dai ya rage zango ne don kar kadaici ya ishe shi, ke din dai wata aba ce ta debe kewa ba matar da za a aura ba, ko kuwa akwai wasu abubuwa da yake hangowa dake sanya shi wasiwasi.
Cikin wadannan dalilai da zan lissafo dole a samu biyu ko uku da za ki ga yana aikatawa wadanda zasu wayar miki don ki fahimci abinda ake ciki.
Duk namijin da ma ke sonki da aure ai yardar iyayenki ne abu na farko da ya kamata yayi don neman izinin aurenki, kafin soyayya ta rufe miki ido ya zamanto ba mutum bane nagartacce da ya dace da rayuwarki har ya zamo abokin rayuwa a gare ki.
Don haka, duk namijin da ba sonki yake da aure ba, sai ya nuna wasu alamomi da za su nuna mi ki cewa ba aurenki zayyi ba. Ga su nan kamar haka.
1. Yana tunanin ba za ki iya zama abokiyar rayuwa a gare shi ba
Yana daya daga cikin dalilan da ya sa ba zai iya tunkarar iyayenki ba, ko kuma ya gabatar dake ga iyayen shi a matsayin matar da zai aura, yana tunanin ba ki dace da zama abokiyar rayuwarshi ba.
Kamar yadda na fada daga farko matukar namiji na son abu ya kan yi iya bakin kokarin sa wajen ganin ya mallaki wannan abu, to daga zarar duk batun babu maganar turo iyaye a yi maganar aure ki sa a ranki cewa ba ki daga cikin tsarin macen da yake son rayuwa da ita.
Kamar yadda wata baiwar Allah da na tattauna da ita ta bani labarin yanda ta shafe shekaru hudu tana soyayya da saurayinta, amma kawai rana tsaka sai taga katin aurensa da wata daban.
"Tun da na fara soyayya da shi bai taba nuna man zai turo magabatansa a yi maganar aure ba, hasali nuna mun yake ni yarinya ce in bari in idar da karatuna. Har sai da na je bautar kasa na matsa ya turo yace in gama bautar kasa tukunna, kwatsam sai ga katin aurensa, hakan ya girgiza ni".
Irin hakan na faruwa sosai, sai dai har yanzu matan sun kasa hankalta da ire-iren wadannan samari.
2. Daga lokacin da soyayyarku ta zama zafi da sanyi
Ma'ana akwai lokacin da za a ganku tare, kafin a ce wani abu kuma kun rabu. Hakan ba zai hana kuma gobe ku dawo ba. Babu takamaimai tsayayyar soyayya a tsakanin ku, kullum tana cikin halin kunnawa da kashewa. Babu ta yadda za a yi ya turo iyayensa a wannan halin da soyayyar ku ke ciki na rashin tabbas. Don haka, matukar ta na rawa, ba zai so maganar aure ta hada ku ba ko kuwa ya turo iyayensa gidanku. Yana da kyau a cikin irin wannan hali, ku samu matukar natsuwa don fahimtar bambance-bambancen da ke tsakanin ku da kuma tattauna su.
3. Rashin tabbas akan halayyarki
Kowane namiji na son ya kai ma iyayen shi matar da zai aura ta zama ta gari kuma mai natsuwa. Matukar akwai rashin daya daga cikin wadannan, duk son da ke tsakanin ku ba zai iya sada ki da iyayen shi ba, bare har ayi maganar aure, saboda bai dauke ki a matsayin mata ba, kuma uwar da yake tunanin za ta kula da tarbiyar yaransa.
Kullum za ki yi ta surutun wane yaushe za ka turo iyayenka? Amma shiru daga ya ce miki yau ko gobe, amma babu wani labari. Ki binciki halayyar ki da bai so, don ba zai so ya kai abinda za a yi Allah wadai da shi ba; zai so ya kai macen da iyayensa zasu yi alfahari da kasancewar ku tare.
4. Akwai yiwuwar bai mance da soyayyarsa ta baya ba, ko kuma akwai wacce yake so ko kuma ma akwai wadda iyayenshi suka san da zamanta
Mantawa da kuma cigaba da rayuwa a lokacin da mutum ya samu karayar zuciya abu ne mai matukar wahala musamman idan an yi zama na so da kauna mai cike da ababen tunawa. To a irin wannan lokacin wani zai ga yin wata budurwar ne maslaha. Sai tafiya ta mika ya fahimci ke ba irin budurwar sa ta baya bace, ba ki dace da irin rayuwar da yake tunanin samu ba.
Dama ya shigo rayuwar ki ne dan ya manta da ita waccen tsohuwar budurwarsa, amma abin yaki ci yaki cinyewa.
Ko kuma ya hango wata wadda yake tunanin ita ce ta dace da rayuwar shi, ba ke ba.
Ko kuma dama can akwai wadda iyayensa suka san da ita. Kin ga kuwa ba yanda za a yi ya gabatar da maganar aurenki wajensu saboda akwai wadda suka riga suka san da maganarta a kasa.
To fa maganar aure ma ba ta so ba, don zai bi duk wata hanya ta ganin ya zille miki, ba tare da ya hadu da iyayen ki ba don neman izini daga gare su. Haka zai yi ta miki yawo da hankali har sai kin gaji kin rabu da shi.
.
5. Dama ya shirya rabuwa da ke ko kuma tun fil azal ba son ki yake ba
Wasu mazan dama ba da niyyar aure suke zuwa ba, sun zo ne da niyyar su rage dogon zango kafin su samu wadda suke so da gaskiya. Ke aikin ki shine faranta masa da kuma rage masa tsawon lokuttan shi.
Ta yiwu kuma a farko yana son ki amma daga baya karsashin ya ragu sosai, kawai lokaci yake jira na rabuwa da ke ya kama gabansa. Ga irin wannan namiji, ko mi za ki yi, ba zai turo iyayensa gidanku ba. Idan kika takura to zai fara ja da baya, za ki rage jin sa da kuma ganin sa, duk wasu abubuwa da yake miki a da zai rage su koma ya daina gaba daya har sai ya zamanto kin neme shi kin rasa; ya tafi. Saboda ba shi da ra'ayin auren ki, ya kan iya miki dadin bakin ba dan baya son ki bane yasa haka, iyayensa na da wacce suke so ya aura ko kuma ya kawo ma ki wani dalilin na daban na rashin turo da iyayensa da bayyi ba.
6. Ba ki daga cikin zabin da iyayensa zasu aminta da ita
Da yawan iyaye kan nuna ma yaransu irin mata ko namijin da suke so su aura. Kowane bangare burinsa ya kawo abinda iyayensa zasu yi farinciki da sam barka a kanta ko kanshi. Babu wanda zai so ya bakanta ma wadanda suka fi soyuwa a zuciyarsa fiye da kowa.
A zaben matar aure da ma sauran harkokin rayuwa iyaye na taka muhimmiyar rawa wajen zaben wadannan ababen ga rayuwar yaransu. To matukar ya san iyayensa ba zasu yi maraba da ke ba a matsayin matar dansu, to ba zai fara tunanin kawo maganar aurenki ba. Har sai zuwa lokacin da kuka rabu za ki fahimci hakan.
7. Bai dauki soyayyarku da muhimmanci ba
Watakila ke yanda kike tunanin soyayyar ku ta kai ko kuma ma ta wuce, shi a wajen sa ba haka ba ne. Kila kina tunanin ta kai wannan matsayin na iyayenku su san da zamanta, sam a wajen sa ba ta da wannan muhimmancin. Ke a wajen ki a shirye kike da ki zama matarshi wanda a wajen sa ba haka abin yake ba. Kowane dan adam da yanayin karfin soyayyar sa.
Matukar namiji ya budi baki cewa zai turo iyayensa, ki sa a ranki cewa ba wai a matsayin budurwa yake kallon ki ba, a'a yana kallon ki ne a matsayi mata kuma uwar yaransa saboda daukar soyayyar da yayi da muhimmanci.
Wanda kuma bai dauke ta da muhimmanci ba, baya ma tunanin tafiyar da soyayyar zuwa mataki na gaba, saboda da ita da babu duk daya suke a wajensa.
Abu na karshe da za ki sani shine, namiji ya turo iyayensa gidanku, ba abu ne da zai faru cikin kankanin lokaci da zarar kun fara soyayya ba. Hasali ma dai akwai bukatar ki yi kaffa-kaffa da namijin dake saurin miki dadin bakin cewa zai turo iyayensa gidanku. Duk abinda kake so na hakika, ka kan dauki lokaci don lura da gamsar da rayuwarka cewa lallai fa wannan abu shi ka ke so kuma ya dace da kai.
Aisha chuku
© Sirrinrikemiji
Post a Comment