Musulmai daga sassan duniya na ci gaba da yin caa kan babban limamin jami'ar Al Azhar ta kasar Masar,Cheikh Ahmed Al Tayib wanda ya ce, yi wa mata kishiya zalunci ne.

A cewarsa wannan babban shehin,a yawancin lokuta mutane na auren mata fiye da daya ba tare da sun hafimci ka'idojin da Al Kur'ani ya gindaya ba.

Mu'addibin ya furta wannan kalamin a wani shirin talabiji da kuma kan shafinsa na sada zumunta Twitter.

Abinda yasa Musulmai daga sassa daban-daban na duniya suka yi caa kansa,amma nan take jami'ar Azhar ta mayar da martani,inda ta ce shugabanta bai haramta abin da Allah (SWT) ya hallata ba.

Limamin ya ce : "Zama da mace daya shi ne daidai.Auren mace fiye da daya wani kebebben lamari ne na dole".

Cheikh Tayeb ya ci gaba da cewa,"Wadanda ke cewa auren mace fiye da daya wajibi ne,ba su da gaskiya.Al Kur'ani mai tsarki ya bayyana cewar, Musulmi ba zai iya auren mace fiye da daya ba face zai ya zama adali.Tilas ne mu kula da mata,saboba sun kasance rabin al'umarmu Musulmai.",inji
Tuni dai matan kasar Masar da na sauran sassan duniya suka jinjina wa babban limamin na jami'ar Azhar.

TRThausa.

Post a Comment

 
Top