Mai taimaka wa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje kan harkar tsara birane, Hashim Dungurawa, ya mika takardar hakura da aiki da gwamnatin inda ya ce zai koma jam’iyyar PDP.

Dungurawa ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da aiki da jam’iyyar gwamna mai ci ba sannan ya gode wa gwamnan bisa damar da ya bashi na yin aiki tare da shi. Tuni ya kammala shiri tsaf domin komawa jam’iyyar PDP

an ba a manta ba jihar Kano na daga cikin jihohin da za a gudanar da zaben a ranar 23 ga watan Maris.

Sauran jihohin da ba a kammala zaben gwamnan ba sun hada da Jihar, Filato, Bauchi, Adamawa, Sokoto da jihar Benuwai.

A jihar Kano abin yayi zafi da sai da aka rika kai ruwa rana tsakanin magoya bayan manyan jam’iyyun da ke fafatawa a zaben, wato APC da PDP.

A dalilin haka sai da ‘yan sanda suka tsare mataimakin gwamnan jihar Nasir Gawuna da kwamishinan Kananan hukumomin jihar, Sule Garu. Daga baya an sake su.

A sakamakon da aka riga aka bayyana, jam’iyyar PDP ce ke kan gaba da kuri’u sama da Miliyan daya.

An bayyana cewa kuri’un da aka soke sun fi yawan kuri’un da jam’iyyar PDP ta baiwa APC rata shine ya sa zaben bai kammalu ba.

Premiumtimeshausa.

Post a Comment

 
Top