Sarkin Kano ya jinjinawa kwamishinan 'yansandan jihar


Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ll ya yi kira ga al'ummar Kano da su zauna lafiya kuma su kwantar da hankali da kuma kiyaya yada jita jita.

Wannan kiran na zuwa ne bayan da aka gudanar da zaben gwamnoni da kuma 'yan majalisar jiha a fadin kasar a ranar 9 ga watan Maris.

Sarkin ya bayyana cewa hukumar INEC ce kadai ke da 'yancin bayyana sahihin sakamakon zabe, inda hukumar ta bayyana cewa zaben bai kammala ba, kuma akwai wasu mazabu da za a sake zabe a jihar.

Daga nan, sarkin ya yi godiya ga Kwamishinan 'Yan Sandan jihar CP Mohammed Wakili da sauran jami'an tsaro musamman kan irin rawar da suka taka wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.

Daga nan, sarkin ya yi godiya ga Kwamishinan 'Yan Sandan jihar CP Mohammed Wakili da sauran jami'an tsaro musamman kan irin rawar da suka taka wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.

Tun bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da cewa zaben jihar bai kammala ba, ake samun fargaba a jihar.

Jigga-jigan manyan jam'iyyun jihar Kano, Ganduje da Kwankwaso sun nemi jama'ar jihar da su zauna lafiya.

Hakan na zuwa ne a ci gaba da zaman dar-dar da ake yi a cikin jihar lokacin ake jiran sakamakon zaben a ranar Litinin.

A ranar Lahadi ne wasu magoya bayan wasu 'yan takara suka fara murnar lashe zaben, wanda hakan ya sanya rundunar 'yan sandan jihar ta yi gargadi da a daina, kuma a jira hukumjar zabe ta bayyana sakamako.

Babban jami'in tattara sakamako zabe a Kano Farfesa B.B Shehu ne ya sanar da cewa ba a kammala zabe a Kano ba, a ranar Litinin.

Ya ce Abba Kabir Yusuf na babbar jam'iyyar hamayya PDP ya samu kuri'a 1,014,474 yayin da gwamna mai ci na jam'iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje ya samu kuri'a 987,819.

Jam'iyyar PRP ce ta zo a matsayi na uku da kuri'a 104,009.

An ki bayyana wanda ya lashe zaben ne saboda bambancin kuri'un da ke tsakanin manyan 'yan takarar ba shi da yawa.

Abin da ya sa dole a sake zabe a wasu mazabu da tun da farko aka soke su.

Hukumar INEC dai ba ta bayyana ranar da za ta sake gudanar da zabukan ba tukuna.

BBChausa.

Post a Comment

 
Top