Rundunar tsaro ta 'yan sanda ta tabbatar da harbe wani dan majalisar wakilai na tarayya a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Wasu mutane ne da ba a sani ba suka harbi dan majalisar a wata rumfar zabe a karamar hukumar Lagelu cikin garin Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Rahotanni sun ce ya mutu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan bayan mummunan raunin da ya samu daga harbin a kai zuwa idonsa.

Babu dai wani karin bayani daga 'yan sanda ko an kama wadanda suka harbi dan majalisar mai suna Olatoye Temitope Sugar


Dan majalisar ya sha kaye a zaben 'yan majalisar wakilai bayan ya nemi yin tazarce karkashin jam'iyyar ADP.

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya yi Allah wadai da kisan dan majalisar wanda ya bayyana a matsayin rashin imani tare da yin kiran a kaddamar da bincike domin gano wadanda suka aikata kisan.

©BBCHausa

Post a Comment

 
Top