Jagoran jam'iyyar PDP a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce duk da ba su gamsu da matakin da hukumar zabe kasar ta dauka ba na sake gudanar da zabuka a wasu jihohin kasar, a shirye su ke su shiga domin a fafata da su a zaben da a sake a wasu yankuna na jihar ta Kano a ranar 23 ga watan Maris, 2019.
A cikin wata hira da ya yi da BBC, sanata Kwankwaso ya ce, ba wani abu ne ya sa ba su amince da sakamakon zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris ba, illa su a fahimtarsu kamar sakamakon kamar akwai zalunci a ciki saboda suna ganin kamar hukumar zabe na da dokoki guda biyu, wato dokar Kano ta 'yan adawa ko kuma wadanda ba a so, da kuma dokar da suka ga ana aiki da ita a wasu jihohi kamar jihar Ogun.
Ya ce dokar da hukumar zabe ta ce idan yawan kuri'un da dan takara na daya samu ba su kai yawan kuri'un da aka soke ba, to sai an sake zabe.
Sanata Kwankwaso ya ce ' Mun ga a jihar Ogun ba haka aka yi ba sai a Kano a kayi hakan'.
Jagoran jam'iyyar ta PDP a jihar Kano ya ce, bisa la'akari da yadda suka ga abubuwa na tafiya a wannan zabe da za a sake a wasu wurare a jihar, to za su dauki mataki domin kuwa za su tabbatar da cewa dukkanin akwatunan da za a jefa kuri'a a cikinsu ko da sau 100 za a jefa, to dan takararsu ne zai samu nasara a kansu.
Don haka ya ce ' Za mu dauki matakanmu ne bisa tsarin bin doka da oda da kotu, don tabbatar da cewa an zauna lafiya a jihar Kano, kuma ba a kyale tinkiya ta haifi kare ba'.
Sanata Kwankwaso, ya ce yakamata su shugabannin su dauki misali a wajensu, kamar lokacin Marigayi Muhammadu Abubakar Rimi, an yi zabe ya fadi zai yi kashi na biyu ya hakura, haka shi ma da kansa ya na neman tazarce a karo na biyu a matsayin gwamnan Kano ya fadi ya hakura har ma ya taya wanda ya ci murna.
Ya ce, su wajensu ba su da wata fargaba a game da zaben da za a sake a wasu wuraren jihar, domin kuwa su sun san sun riga sun ci zabe.
BBChausa.
Post a Comment