![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjxj3_YZ5sTRR3kbNjt1yhZAPetOl7H2zN5bhkY2mv2gKHU85_7wfmgAo8rQppZbeEFBXhm5lQ_ErLKyobvhAXJW6oTcrMx_B3nCHZQJRy-6BvWn21GeBRHr7TFWZ8gvgrP2qysNAzpKAHH/s1600/ic-3540.jpg)
Jarumar fina-finan Hausa, Ummi Abdulwahab wadda aka fi sani da Ummi Duniyarnan ta samu ladar aiki me tsoka daga gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari bisa wakar da ta mai.
A wani bidiyo da ta wallafa a dandalinta na sada zumunta, anga kudi kimanin miliyan 6 da dubu dari 5 wanda aka saka a asusun ajiyarta na bankin Ja'iz kuma za'a iya jin wata murya na magana a cikin bidiyon inda tace kudin ladar wakar da Ummin ta yiwa gwamnan Katsinane da ya bata, watau Aminu Bello Masari.
A sakon godiya data fitar, Ummi tace ta godewa Allah sannan kuma ta godewa Me gidanta, Nasir Gwangwazo bisa nuna mata hanyar samu da yayi
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEj9mMJdzlxBKnvsFwZAzdgPO1PF_R1GUBKxpodgutga_ezvPQRWGsGFlokHp1xdt4ISKPH6A_WxrZ22BlC_EBFOj0i4Ud2azJFuaM5Cvk2rxJQeljQq9NyqAmyww3xYTpOo-QPuhS_BYHjy/s1600/ic-2549.jpg)
Danna Nan Domin Kallon Videon
Post a Comment