Bayyana sakamakon zaben gwamna a jihar Kano ya samu tsaiko yayin da ake jiran sakamakon karamar hukumar Nasarawa, wanda shi kadaine ya rage ba'a fada ba cikin kananan hukumomi 44 na jihar a yayin da PDP ke gaba da tazarar da babu yawa. Saidai INEC ta ce an kekketa sakamakon.

Kwamishinan zabe na jihar, Riskuwa Shehu ya bayyanawa 'yan jaridu cewa a yayin da suke jiran sakamakon karamar hukumar Nasarawa sun samu rahoton cewa an samu yamutsi wajan hada sakamakon inda har saida 'yan sanda suka kwaci wasu manyan mutane daga hannun 'yan bangar siyasa bayan da aka yaga takardar sakamakon.

Ya kara da cewa, shi kanshi jami'in INEC din dake karbar sakamakon karamar hukumar Nasarawar sai da aka kwaceshi daga hannun mafusatan amma ya kara da cewa babu abinda ya sameshi.

Yace zasu yi amfani da wasu hanyoyi wajan tattara sakamakon na jihar Nasarawa, kamar samun sakamakon daga mazabu da sauran su sannan zasu yi amfani da na'urar tantace masu zabe wajan karbar sakamakon, ya kara da cewa, zasu yi amfani da dokokin hukumar wajan amincewa ko kuma kin amincewa da sakamakon da be kamataba.

Post a Comment

 
Top