Mu yi hakuri mu jira zagaye ta biyun da za ayi, InshaAllah za mu yi nasara Inji Abba Yusif kabeer.


Dan takaran gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP Abba Yusuf ya roki magoya bayan sa da su yi hakuri a jira a kammala zaben jihar Kano da aka bayyana bai kammalu ba.

A cikin takarda da ya fitar wanda kakakin sa Sanusi Dawakin Tofa ya saka wa hannu, Abba ya bayyana cewa idan suka yi hakuri komai zai zo ya wuce.

” An san mu da hakuri. Mu ci gaba da yin haka in Allah ya yarda muna a sama ko bayan an kammala zaben. Sannan kuma magoya bayan mu su sani cewa PDP ce ke kan gaba a sakamakon da aka bayyana mune a kan gaba kuma inda ma za a sake zabukan dun wuraren da muke da karfi ne aka soke.

” Ina kira ga wuraren da aka samu wadannan matsaloli da za a sake zabe su fito kwansu da kwarkwata su zabi jam’iyyar PDP a zaben.

Post a Comment

 
Top