A kasar Malaysia kotu ta yanke wa wani gafalalle da ya yi batanci da Addinin Musulunci da Annabi Muhammad Sallallahu Alai Wa Sallam daurin shekaru 7 a gidan yari da kuma biya biyan tarar dala dubu biyu da 445.

A ranar 4 ga watan Maris ne mutumin mai suna Muhammad Yazid Kong Abdullah ya yi rubtun na batanci a shafin sadarwa na sada zumunta kuma a ranar Juma'ar da ta gabata ya amsa laifinsa wanda hakan ya sanya aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 7 da tarar dala dubu 2,445.

A ranar Asabar din da ta gabata ma an yanke wa wani mutum daurin shekaru 10 a kurkuku bisa kalaman batanci ga Annabin Tsira Muhammad (SAW) a kasar ta Malaysia.

Rundunar 'Yan sandan Malaysia ta bayyana cewa, a 'yan watannin nan ana yawan samun karuwar yin kalaman batanci ga Musulunci da Annabin Rahma a kasar a shafukan sadarwa na sada zumunta inda ya zuwa yanzu aka kai musu korafi har sau 929.

A watan da ya gabata a kasar wani dan kasar China ya yi wa Annabi Muhammad batanci a shafin sadarwa na sada zumunta wanda hakan ya sanya aka kama shi, kuma wasu sun gudanar da zanga-zanga a birnin Kula Lumpur.
TRThausa.

Post a Comment

 
Top