Bayan kammala zaben shugaban kasa dana 'yan majalisar dattijai dana wakilai da ya gudana ranar Asabar din data gabata kuma hukumar zabe, INEC ta bayyana cikakken sakamko, wasu 'yan siyasa sin ci riba yayin da wasu suka tafka asara, wasu kuma dake kan kujerunsu guguwar zaben ta yi gaba dasu.
Atiku Abubakar.
Mutum na farko da ya tafka babbar asarar da tafi ta kowanne dan siyasar da aka yi wannan zaben dashi shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, domin kuwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya tikashi da kasa, duk da dai cewa yayi rawar gani, lura da yawan kuri'un da ya samu.
Bukola Saraki.
Mutum na biyu da ya tafka asara a zaben 2019 shine kakakin majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki. Sataki ya jima baya ga maciji da fadar shugaban kasa wadda dalilin haka tasa ya canja sheka daga APC zuwa PDP, ga kuma tsamar dake tsakninshi da ministan labarai, Lai Muhammad wanda suka fito daga jiha daya, ga kuma zargin da ake mai da hannu a daukar nauyin 'yan fashin da suka kai hari Offa, Saraki ne sanata na farko da aka fara tabbatar da faduwarshi a zaben 2019.
Shehu Sani.
Sanata Shehu Sani na jihar Kaduna shine na uku a jerin wanda suka tabka babbar asara a zaben 2019, tun zaman Shehu Sani sanata me wakiltar Kaduna ta tsakiya suka kulla tsama da gwamnan jihar Kadunan, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai wanda har Gwamnan yayi zargin cewa Sanatan tare da hadin kan sanatocin jihar sun hana jihar cin bashin kudin da za'awa al'umma aiki da gangan, wannan yawa Sanata Shehu Sani wanda ake kira da me gashi bakin fenti a wajan talakawan jiharn, bayan kammala zaben Uba Sani na hannun damar gwamnan Kadunane ya dada Shehu Sani da kasa, ya fado taka, dan kuwa a na uku yazo. Kuma zango daya kawai yayi a majalisar.
Karanta Wannan: Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Inji Sheikh Ahmad Gumi
Godswill Akpabio.
Sanata Godswill Akpabio wanda tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom ne kuma tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai wanda ya ajiye mukamin nashi ya kuma koma jam'iyyar APC ya kuma tsaya takarar sanata a jam'iyyar shima ya fadi zabenshi, duk da shi ana mai kallon cewa watakila ya samu mukamin siyasa Amma duk da haka ya tafka asara.
Gwamna Ibrahim Dankwambo.
Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo na daya daga cikin manyan 'yan siyasar da suka tafka Asara a zaben 2019, gwamnan wanda kwanannan zai zama tsohon gwamna ya fadi zaben sanata da ya tsaya wanda ba kasafai hakan take faruwa ba, wasu masu sharhi dai sun alakanta hakan da yin Sak da masu kada kuri'a suka yia jihar.
Barnabas Bala Bantex.
Mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Barnabar Bala Bantex wanda ya bar mukamin nashi na mataimakin gwamna ya tsaya takarar sanata a kudancin Kaduna ya sha kasa, yayi biyu babu.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kalli Wannan: MURNAR CIN ZABEN BUHARI: Yadda ’yan acaba su ka rikita wasu sassan Abuja
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda dama bai tsaya takara ba amma ya tsayar da dan takara kuma ya fadi, babban abin daukar hankalin ma shine Toshon gwamnan Kano wanda ya taba kadashi a takarar gwamna, Malam Ibrahim Shekaraune ya kada dan takarar na shi kuma zai kwace kujerarshi ta sanatan, sannan kuma dan takararshi na shugaban kasa, Atiku Abubakar shima ya fadi, wanda ko karamar hukumarshi ta Madobi be kawomai ba.
©HTDL
Post a Comment