Aure ya zama tamkar wasan yara a wajen Malam Bahaushe saboda rashin martaba shi da ba a yi.

Sau tari za ka samu da an fara zaman soyayyar ta ke gushewa sabida ma’auarantan na kasa kiyaye wasu ginshikan soyayya da ke habaka kauna a zukatan juna.

Da zarar an fara samun matsaloli nan da can kuma sai ka ga duk an fara gundurar juna. Sai danganta ta yi tsami. Sai rashin kyautatawa ta biyo baya, daga nan kuma sai ka ji ko dai mijin ya furta saki, ko kuma matar ta nemi a saketa saboda zaman ya ki dadi.

Wadannan hanyoyi guda 38 in aka bisu sau da kafa za su dawwamar da soyayyar mata a zuciyar mijinta.

1. Ka zamo mai tausasa zance a gareta, kar ka zamo mai yawan fada.

2. Idan ka shiga gida kace ‘Assalamu Alaikum’, sallam tana korar Shedan daga gida.

3. Annabi SAW yace mata kamar kayan qarau ne saboda haka kula dasu sosai, ka tuna akwai alkhairi a cikinsu saboda haka sai a tarairayesu.

4. Idan zaka bata shawara ko zaka yi mata fada ya zamo a cikin sirri, wato alokacin da kuke ku kadai, kada ya zamo a cikin mutane dan yin hakan muzantawa ne.

5. Ka zama mai kyautatawa matarka, hakan yana qara soyayya.

6. Idan tazo zata zauna ka tashi ka bata wurin zamanka, hakan zai tausasa zuciyarta.

7. Ka guji yin fushi ta hanyar riqe al’wala a koda yaushe. Annabin Rahma SAW yace idan kayi fushi to idan a tsaye kake sai ka zauna, idan a zaune kake sai ka kwanta.

8. Ka rinqa yin ado kana sa turare saboda ita.

9. Karka zamo mai tauri, Annabi SAW yace : ‘Nine mafi kyautatawa zuwa ga iyalina’, idan kayi tauri da yawa baza ka samu kusanci zuwa ga Allah ba, haka kuma baza ka zamo namiji jarumi ba.

10. Ka dinga sauraron duk abinda matarka zata gaya maka koda kana ganin abin bashi da muhimmanci, hakan zai sa ta san ka damu da ita.

11. Ka kaucewa cin musu da matarka, yana kawo rabuwar kai.

12. Annabi SAW yace ku kira matanku da sunaye masu dadi, sunan da suke so suji ka kira su dashi.

13. Ka riqa yi mata tsarabar bazata, idan tana sha’awar wani abin marmari sai ka sayo mata ba tare da ta sani ba.

14. Ka kula da harshenka zuwa gareta, wato ka guji abubuwan da zasu sa ta fushi.

15. Mutum tara yake bai cika goma ba, kayi haquri da duk wani aibun da take dashi sai Allah SWT ya sa albarka a cikin auren naka.

16. Ka dinga nuna mata yabo da godiya idan tayi maka abu mai kyau.

17. Ka dinga taimaka mata wajen ganin ta kula da dangantakar ‘yan’uwanta da iyayenta.

18. Ka yawaita janta da hira akan abinda take so.

19. Idan kaga ‘yan’uwanta suna kusa, ka dinga yabonta, kana kambamata, kana tabbatar musu da kirkinta da kyautatawarta.

20. Ku dinga yiwa junanku kyaututtuka. Manzon Allah SAW yace kyauta tana qara soyayya.

21. Idan kayi mata laifi sai ka samu wani abu ka kyautata mata dashi dan ya goge laifin.

22. Ka rinqa kyautata zato a gareta, banda zargi!

23. Karka dinga kulawa da qananan laifukanta, kayi kamar baka gani/ji ba. Yana daga cikin ‘dabi’un Sayyidina Aliyyu (RA).

24. Ka nin-ninka haqurinka da ita musamman a lokacin da take jinin al’ada.

25. Ka ringa sauraron zuwan kishinta, kuma ka ringa yabon kishin nata, ko manta Manzon Allah SAW suna kishi!

26. Ka zamo mai qasqantar da kai, idan ka zamo mai tunani to ka tuna cewa tana kula da ‘ya’yanka, itace mai kula da gida!

27. Karka dauki abokanka sama da matarka!

28. Ka ringa taimaka mata da ayyukan gida. Manzon Allah SAW ya kasance yana taimakon matansa.

29. Ka taimaka mata wajen girmama iyayenka, baza ka iya takura mata taso su ba amma zaka iya taimaka mata dan ta cimma hakan.

30. Ka dinga nuna mata cewa itace irin matar da kake ta addu’ar ka samu.

31. Karinga tunawa da matarka a cikin addu’o’inka, hakan zai qara qarfin soyayyar taku.

32. Kada ka dinga tunawa da baya, babu abinda hakan zai jawo sai damuwa, abinda ya riga ya wuce a barwa Allah.

33. Karka taba nuna mata cewa taimaka mata kake idan kana mata wani abin kamar sayan abincin gida, saboda a zahirin gaskiya mu ‘yan aikatarwa ne kawai, Allah shine yake azurtawa da ciyarwa. Wannan kuma wata hanya ce ta qasqantar da kai ga Allah SWT da kuma gode masa.

34. Ka gane cewa Shaidan maqiyinka ne amma ba matarka ba, wani lokaci idan mata da miji suna magana idan suka samu sabani sai Shaidan ya shiga tsakani. Kayi iya qoqarinka wajen ganin Shaidan bai shiga tsakaninka da matarka ba.

35. Ka ringa bata abinci a baki, Annabin tsira SAW ya koya mana hakan, abincin ba wai iya cikinta zai tafi ba idan ka bata a baki, har zuwa cikin zuciyarta.

36. Ka kare matarka daga duk wani sharri ta hanyar yi mata addu’o’in neman tsari.

37. Ka zamo mai yawan yi mata murmushi.

38. Ka guji duk abinda bata so ko mai qanqantarsa, idan baka kula ba ta haka ne zai girma har ya zama babba.

Post a Comment

 
Top