Ga dukkan alamu dai sakamakon zaben jihohin Borno da Yobe na ci gaba da daukar hankula sosai kuma be yiwa musamman 'yan kudu dadi ba, bayan zagin da suka gama yiwa 'yan Arewa a shafin Twitter akan sakamakon jihohin biyu, mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Peter Obi ma ya fito yace sakamakon jihohin biyu akwai rainin hankali a tattare dashi.

Peter Obin ya bayyana hakane a gidanshi dake Onitsha yayin wata ganawa da yayi da manema labarai, kamar yanda The Nation ta ruwaito, inda yace da gangan aka shirya hana mutanen yankinshi yin zabe yanda ya kamata domin ta yaya za'a ce yankin nashi na kudu maso gabas dake da masu zabe miliyan 10 ace kwata-kwata kashi 20 ne cikin 100 kawai suka samu jefa kuri'a?

Yace idan za'a iya tunawa, a ranar zaben ya bayyana cewa akwai matsala domin na'urar tantance katin zabe bata yi aiki yanda ya kamata taba dan haka mutane da yawa basu samu damar yin zabe ba.

Yace tun lokacin da na'urar zabe 400,000 ta kone suka san cewa akwai matsala kuma INEC ba ta yi wani abu dan warware matsalar ba sannan kuma tace ba zata baiwa mutane dama su yi zabe bada na'urarba.

Amma a wasu yankunan kasarnan an baiwa mutane dama sun yi zabe ba tare da amfani da na'urar tantance katin zabe ba kuma INEC din ta amince da sakamakon, yace shin wai ta yaya za'a ce mana jihohin Borno da Yobe sun kawo kuri'un da suka fi na jihar Anambra da Ebonyi yawa?

Wadannan jihohi biyu yaki kawai ake ta bugawa a ciki, to ta yaya aka yi suka samu na'urar tantance zabe da ta yi aiki yanda ya kamata duk da yakin da suke ciki? Abinfa akwai ban mamaki.

Ya kuma kara da yin Allah wadai da yanda aka gudanar da zaben inda yace maimakon a samu ci gaba akan zaben 2015 sai ma ci baya aka samu sannan yace jami'an tsaro sun wulakanta 'yan jam'iyyarshi

Post a Comment

 
Top