Da kunne na na ji an tambayi Shugaba Buhari idan ya ci zaben shugaban kasa bayan ya gama wa yake so ya gaje shi akan mulki? Buhari ya ce Kwankwaso.

Shugaba Buhari yana wannan magana ne lokacin da aka yi zaben fidda gwani na Jami'yar APC a shekarar 2015, Buhari ya lashe zaben lokacin Kwankwaso yana cikin jami'yyar kuma shine ya yi na biyu a zaben fitar da gwanin.

Abin tambaya a nan shin shugaba Buhari yana kan wannan magana har yanzu ko kuwa tunda sun raba jami'yya shike nan?

Ni dai bisa harsashen siyasa da na yi akwai yuwuwar Kwankwaso zai sake komawa jami'yyar APC musamman idan suka yi nasarar kayar da APC a zaben gwamanan Jihar Kano amma fa idan bukata ba ta biya ba to lissafin siyasar Kwankwaso ya shiga tsilla- tsilla.

Abin Jira Mu Gani Lokaci.

Daga Ibrahim Rabiu Kurna.
Rariya.

Post a Comment

 
Top