Shugaban jamiyyar PDP a jihar Katsina Kuma dan takarar mataimakin Gwamna a karkashin jamiyyar adawa ta PDP, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya bayyana matsayar jamiyyar sa ta PDP inda ya ce jamiyyarsa ba ta amince da zaben shugaban kasa ba, da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, sakamakon Magudi da kura_kura da aka tafka a cikinsa.

Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala tattara sakamakon zaben Shugaban kasa da aka gudanar a helkwatar Hukumar zabe ta kasa reshen jihar Katsina.

Majigiri ya cigaba da cewa mun zauna tattara sakamakon zabe na tsawon awa arbain da takwas, Kuma sakamakon zabe ya gwada mana har yanzu akwai sauran rina a kaba, akan tsarin zabe a kasar nan, mun lura zaben cike yake da tuntube da kura kurai da magudin zabe. Wannan dalili ya sa ba mu sa hannu ba kuma ba mu gamsu da yadda aka gudanar da shi ba.

Shugaban jamiyyar ya kara da cewa misali a karamar Hukumar Kankara, takardun da aka amshi sakamakon zaben da su, ba su ne takardun da hukumar zabe ta amince da su ba ko ta tsara yin aikin zabe da su ba a 2019. Har ila yau, sakamakon da aka bayyana yana cin karo_da_juna, an tantance Mai jefa kuria adadi kaza, amma sakamakon yana zarta yawan wadanda aka tantance, ka ga daga sama suka zo ko daga kasa ba mu sani ba

Da aka tambaye shi wane mataki za su dauka, ya kada baki yace na farko dai ba mu yadda da sakamakon ba, Kuma ba mu aminta da shi ba, saboda kwamacalar da ke cikinsa, duk cigaban da jamiyyar mu ta samu idan muka kwatanta da zaben 2015.

Saboda 2015 jamiyyar APC ta samu Miliyan Daya da dubu dari ukku, yanzu ta rikito da Miliyan daya da dubu dari biyu. A 2015 jamiyyar mu ta PDP ta samu kuriu dubu tisin da takwas, yanzu mun samu dubu dari ukku da wani Abu kaga mun samu gagarumin cigaba. Duk da hakan da an yi sahihin zabe kamar wanda muka Yi a 2015, ba tare da an Yi amfani da wasu abubuwa na gwamnati ba, da sakamakon ba haka zai nuna ba.

Idan za a iya tunawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben da gagarumin rinjaye inda ya samu Kuriu Miliyan Daya da dubu dari biyu, inda Atiku Abubakar ya samu Kuriu dubu dari ukku a jihar Katsina.

Rariya.

Post a Comment

 
Top