A safiyar yau Laraba dandazon ‘yan acaba daga garuruwan da ke gefen Abuja, sun cika wasu sassan birnin inda a yanzu haka su ke ta bulkara, tukin ganganci da mashalo a kan titinan Birnin.

Ba wani abu su ke ba, sai karya dokar birnin wadda ta haramta yin acaba a ciki, su na sagarabtun murnar sake lashe zabe da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Wakilin PREMIUM TIMES HAUSA da ya gane wa idon sa abin da ke faruwa, ya ga yadda masu baburan suka cika babban titin Samuel Ladoke Akintola, da ke Garki, su na ta hauka da babura.

Baya ga gudun tsiya da tukin gangancin da su ke yi a bangaren titin duka biyu, su na kuma buga ‘knock out’ mai firgita jama’a.

Da dama sun a tsammani bindiga ce ake harbawa ta na tashi kamar sau hudu ko sau biyar a lokaci daya.

Wani dan acaba mai suna Garba, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa, “ba bindiga ba ce mu ke harbawa.
‘Knockout’ mu ke hadawa da burkin babur. To da mun taka burki, sai ka ji kara daram! Da mun sake takawa sai ka kara jin daram!”

Ya zuwa 12:15 na rana kuma, zanga-zangar murnar ta kara tsamari, inda matasa masu kanana saide-saide kamar lemo, kankana, masu wankin takarmi da masu dako a Kasuwar Garki Market da sauran ‘yan cirani da ke cikin Garki Village, duk sun bi sahun bulkarar da masu Babura ke yi a kan titina, ana tafiya ana wake-waken APC.

Wata zugar matasa tantagarya ta wuce a kan titi, inda motar da suke tafiya tare da su ke motsawa a hankali, su na tafiya tare da wata rindimememiyar motar da aka daura wa manya-manyan lasifiku na zamani, kuma aka nade ta kaf da fastar Baban Chinedu, ta na fidda kida da wakar Rarara da karfin gaske.

Matasa ne runduna guda biye da motar, kowane ya hunce babu riga a jikin sa, su na tsalle, su na murnar nasarar kayar da Atiku da Buhari ya yi.

Wata mata mai Emmaculate, ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa, ta na mamakin yadda matasan ke saida ran su sun a ta ganganci da Babura, alhali su wadanda su ka ci zaben da ‘ya’yan su na can wuri daya abin su.

Ta ce ai kamata ya yi su gayyato ‘ya’yan wadanda suka yi nasara, sai su yi haukan tare da su.

Su kan su masu babauran Keke NAFEP ba a bar su a baya ba wajen wannan ganganci da ababen hawa.

Su dama tun a ranar Lahadi da safe bayan sakamakon jihar Kano ya fara fita, suka fara ganganci a cikin wasu unguwanni a Abuja.

Wakilinmu ya ga yadda a gaban sa masu baburan A Daidaita Sahu din su ka rika yin ganganci har su na dage tayar baya guda daya, su karkace babur din su na gudu da taya daya.

Duk wannan bulkara su na yin ta ne a kusa da Hedikwatar ‘Yan Sandan Abuja, da ke kallon Kamfanin Buga Kudi na Najeriya, kusa da tsohon ginin Babban Bankin Najeriya, CBN, har zuwa Kasuwar Garki Monday Market zuwa Lagos Street.

Post a Comment

 
Top