Sanata Shehu Sani me wakiltar Kaduna ta tsakiya kuma dan takara a jam'iyyar PRP yayi rashin nasara a zaben daya gudana ranar Asabar data gabata, inda Uba Sani na jam'iyyar APC kuma na hannun damar Gwamna El-Rufai ya dadashi da kasa.

INEC a jihar Kaduna ta bayyana cewa, Uba sanine ya zo na daya da kuri'u 355, 242, yayinda dan takarar PDP, Lawal Usman yazo na biyu da kuri'u 195, 497, Shehu Sanine ya zo na 3 da kuri'u, 70, 613.

Saidai Sanata Shehu sanin tuni yayi fatali da sakamakon zaben inda yace wakilan jam'iyyar su ta PRP da suka tura su duba yanda zaben ya gudana a mazabun jihar ta Kaduna sun tabbatar musu da cewa kashi 90 cikin dari na kuri'un APC sayensu suka yi.

Sannan akwai matsaloli da dama da suka faru a zaben dan haka yana bukatar a sokeshi, ya kara da cewa ya turawa hukumar zabe ta INEC da wannan bukata hade da hujjojinshi, yace a matsayinshi na dan gwagwarmaya inda ace zaben Allah da annabi akayi babu abinda zai hana yayi halin dattako ya amshi sakamako amma a irin wannan murdiya da aka yi bazai amince ba kuma watakila ma yaje kotu.

Post a Comment

 
Top