Kwamishinan 'yansanda na jihar Kano, Muhammad Wakili ya bayyana dalilin da yasa mutane ke ganin kamar yana shan kwaya a wata hira da yayi da jaridar Daily Trust.

Jaridar ta tambayeshi shin yasan cewa dalilin wani bidiyo da ya watsu yana jawabi akan matsalar shaye-sahaye ana mai lakabi da 'Maza Kwaya Mata Kwaya' kuma ya yake ji game da haka?

Wakili yace yana sane da hakan amma be dame shi ba. Yace me zai sa hakan ya dameni? Kowa yana bayyana ra'ayinshine akan yanda ya fahimci abin. Ya kara da cewa, ya ji ma wasu na cewa ni kaina ina shaye-shaye amma hakan ba gaskiya bane.

Kawaidai ina kokarin bayar da gudummuwatace wajan kawar da shaye-shaye tsakanin al-umma saboda nasan irin matsalar da take jawowa.

Da jaridar ta tambayeshi me yasa yake tunanin mutane na cewa yana shaye-shaye?

Sai Wakili yace, Watakila saboda yanda yake magana akan abubuwan da suka farune ko kuma yanayin dabi'arshi.

Su a gurin su ina abune irin na 'yan kwaya amma haka Allah yayini, idan ina magana nakan rika motsa jikina da hannuwana wani lokacin ma in juya wanda hakan ke baiwa wasu dariya saboda basu saba gani ba wanda ni kuma haka Allah yayini.

Yace babu abinda zan iya yi akai, haka Allah ya halicceni, wasu kwayoyi da damama ban san sunayensu ba sai bayan da na shiga aikin 'yansanda.

Post a Comment

 
Top