An bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Najeriya a karo na biyu, abin da zai ba shi damar sake mulkar kasar na karin shekaru hudu masu zuwa.
Shugaban mai shekara 76, na jam'iyyar APC, ya kayar da Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, da tazarar kuri'u kusan miliyan hudu.
Sai dai jam'iyyar adawa ta PDP, wacce Atiku ya yi wa takara, ta yi watsi da sakamakon zaben da Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Mahmood Yakubu ya bayyana da misalin karfe 4.30 na asuba.
Nan gaba kadan ne ake sa ran shugaban zai yi jawabin murna ga magoya bayansa, duk da cewa kawo yanzu abokin takararsa bai mika wuya ba.
Tun a sakamakon farko-farko da aka fara bayyanawa jam'iyyar ta yi zargin cewa akwai kura-kurai a zaben.
An samu jinkiri da kuma tashin hankali gabanin da kuma lokacin zaben sai dai masu sa'ido masu zaman kansu ba su ce an yi magudi ba.
Shugaba Buhari ya yi nasara a jihohi 19 daga cikin 36 na kasar, yayin da babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar ya samu jihohi 17 da kuma babban birnin kasar Abuja.
Buhari ya samu kuri'u 15,191,847, yayin da Atiku ya samu 11,262,978, kamar yadda Hukumar Zabe ta INEC ta bayyana.
BBChausa.
Post a Comment