Jami’in Zabe na INEC mai kula da Karamar Hukumar Bokkos, cikin Jihar Filato, Salihu Musa, ya bada hakuri dangane da abin kwatagwalcin da wani jami’in INEC ya yi, inda ya sha giya yay i mankas.

Musa ya yi ban-hakurin ne a lokacin da ya ke maida amsa ga wata tambaya da ejan na jam’iyyar APC ya yi masa.

Jami’in mai suna Emmanuel Bok, ya yi tambayar ce a Pankshin, inda ya nemi jin dalilin da ya sa shi Musa din ne ya ke fadin sakamakon zabe, maimakon jami’in bayyana sakamako, wato ‘Ruturnin Ofiicer.’

A kan haka ne sai Musa ya shaida masa cewa an sallami jami’in da ya kamata ya bayyana sakamakon, tun a ranar Lahadi, saboda an same shi ya giya ya yi mankas har ya kasa gudanar da aikin sa.

Nan take Musa ya kara bada hakuri a madadin INEC, kuma ya sha alwashin cewa hakan ba za ta sake faruwa ba a nan gaba.

An tabbatar da cewa wanda ya sha gidar dai ya yi mankas, malamin jami’a ne.

A nan take Bok ya ce ya karbi uzirin da Musa ya gabatar. Ya ce amsar da aka ba shi ta yi amfani, domin a baya nufin sa ba zai amince da sakamakon ba, saboda ba shi ne ya dace ya bayyana sakamakon ba.
Premiumtimeshausa.

Post a Comment

 
Top