Masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan makon. Da fatan ana jin dadin abubuwan da muke kawo muku masu matukar amfani a zamantakewarmu na yau da kullum.

Dangane da yawan wayan da nake samu a kwanakin nan, yawanci amare ne suke neman yadda za su yi da fatar su don su yi kyau da sheki a lokacin bikin nasu.

Dama dai kowa ya san amarya da kokarin son birge angonta, bisa sanin amfanin hakan ga amare sai in ce na yo muku tsaraba ta musamman da za ta biya bukatunku.

Bisa bincike ga abin da na fara samowa Insha Allah.

A wani lokaci kuma zan kara turo yadda za a cire baki da ke makalewa a wurare kamar su gwiwar hannu da yatsotsin kafa da hannu da gwiwa da kuma matse matsin cinya Insha Allah.

Amma ga wanan yanzu kuna iya farawa. Ana bukatar abubuwa kamar haka :-

Dilka
Ki samu dilka ki zuba mata ruwan zafi,idan tayi laushi sosai sai ki ajiyeta a gefe.

Kurkum
Ki fasa kwai ki cire yolk din ki zuba kurkur aciki da dan lemon,ki buga sosai ki ajiye agefe.
Dorot
Ki tanadi turaren dorot dinki.
Ki shafe jikinki da wannan kurkur din ko ina,idan ya bushe sai ki dakko wannan dilka din ki goge kurkur din da shi kiyi ta murzawa sai komai ya fita ya yi fes, sai ki samu manja ki shafe jikinki da shi sai ki zuba dorot ki rufe jikinki ruf amma banda kai, idan kika dan jima sai ki fito ki je ki yi wanka, washe gari ba sai kin shafa manja ba, da kin shafa kurkur ki yi turaren idan kin fito ki goge da dilka, haka za ki yi har tsawon kwana hudu, idan baki da pimples ki yi har fuska, idan kina da su in kin gama ki shafa lemon tsami a fuskar.

Kar a manta idan an gama wankan a zuba madaran turare a dan ruwa kadan a watsa a jiki. Za a sha mamaki cikin yardar Allah.

Post a Comment

 
Top