Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya lashe zabe a karin jihohi kamar haka: Ya lashe jihar Naija kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya tabbatar, sannan ya lashe jihar Kogi, da kuma jihar Jigawa inda ya samu kuri'u 794, 738 yayin da shi kuma Atiku ya samu kuri'u 289, 895.

Haka kuma shugaban ya lashe zaben jihar Yobe inda ya samu kuri'u 586,137, yayin da shi kuma Atiku ya samu 50,763.

Ya kuma lashe zaben jihar Gombe da kuri'u 402, 961, yayinda Atiku ya samu kuri'u 138, 484.

Shugaba Buhari ya kuma lashe jihar Kwara da kuri'u, 308, 904 yayin da shi kuma Atiku ya samu 138, 184.

Post a Comment

 
Top