Tsohon sojannan mafi tsufa da ya halarci yakin Duniya na 2, Pa Adama Aduku ya bayar da labarin yanda ya shiga aikin soja da kuma yanda aka yi yaje yakin Duniya na 2.

Aduku dan shekaru 101 da aka haifa a shekarar 1918 a garin Abejukolo-ife dake karamar hukumar Omaha, jihar Kogi wanda su noma ne suka sa a gaba a iyalinsu ya bayyanawa jaridar Punch cewa a shekarar 1942, watarana yana komawa gida daga gona yaga wani Soja me suna, Salikawa yana dukan shugaban kauyensu, wai dan ya ki daukar mai kaya ya kaimai gida.
An kai maganar gaban hakimin yankinsu sai ya baiwa shugaban kauyen shawarar ya bi umarnin sojan ko kuma duk abinda ya faru dashi to ya kuka da kanshi.

Aduku yace wannan abu ya matukar batamai rai inda yasa a ranshi sai ya shiga soja dan ya zo ya ramawa me garinsu dukan da Salikawa ya mai.
Yana dan shekaru 24 ya ya tafi Benue da zummar shiga soja ba dan kawai ya ramawa me garinsu dukan da aka mai ba hadda girmamawa da yake son ganin ana bashi.

Shekaru biyu bayan da ya shiga aikin soja aka dauke su zuwa yakin Duniya na biyu.
Sun tafi zuwa Oyo, daga nan suka wuce Egypt inda suka nufi Bombay, India da kuma Kalkota.
Ya bayyana cewa, kamin su kai Egypt, guzurin ruwansu ya kare saidai ruwan teku me gishiri suka rika sha.
Yace sun yi yaki tare da sojojin Ingila inda suka ci Japan da Burma da yaki.
Yace a shekarar 1946 ya dawo Gida da Fan 100 wanda a wancan lokacin kudi ne masu tarin yawa.

Yace bayan dawowarshine sai ya fuskanci matsi daga gurin kakarshi dake sonshi sosai kan cewa ya bar aikin soja saboda yanda taga ana kashe sojoji da yawa, mata na zama zawarawa 'ya'ya na zama marayu.
Yace hakanan ya bi umarnin kakar tashi ya bar aikin soja.

Daga nanne sai ya shirya ya tafi Legas da niyyar fara kasuwanci da Fan 100 dinnan da aka bashi daga aikin soja.

Yace amma ya gamu da matsala da ta sakashi cikin damuwa sosai, dan kuwa an sace mai fan 100 dinnan a legas.
Na shiga damuwa sosai amma daga baya dole na hakura na koma ina juya dan abinda yamin saura.

Yace a shekarar 1947 ya samu ya ganganda yayi aure a yayin da yake karamar sana'a.
Amma bai natsu da sana'ar da yake ba dan haka ya gayawa matarshi cewa zai koma aikin soja.
Bata mai gadda ba amma sai ta rokeshi ya bari ta haihu tukuna.

Haka kuwa aka yi a shekarar 1950 bayan da matarshi ta haihu sai ya koma aikin soja inda yayi aiki a bangarori daban-daban.
Yace da ya kai shekaru 39 sai ya yanke shawarar barin aikin soja.

Yace bayan da ya bar soja sai 'yar uwarshi ta bashi shawarar komawa gida ya kama aikin gona maimakon kasuwanci, na samu arziki sosai a harkar noma kuma har yanzu ina zuwa gona dan duba ma'aikatana, injishi.
Tsohon sojan da kwanannan mataimakin shugaban kasa ya karramashi, yace yana son shayi wanda kuma yana daya daga cikin sirrin da yasa har yanzu yake da karfi.
Yace a gidansu karfin mazakutar mutum bai karewa har ya mutu.

Dan haka shima duk da yana dan shekaru 101 babu macen da bazai iya gamsarwa ba a gado. Dan hakane ma da yawa matasan mata ke kawomin harin in kwanta dasu, sukan kirani idan na yi tafiya yaushe zan dawo gida?
Amma a matsayina na kitista na gari bana kulasu.

Ya kara da cewa babban abinda ke cimai tuwo a kwarya shine 'ya'yanshi duk sun ki aikin soja, bazan iya tursasu ba amma na basi shawara sun ce basa so.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top