Abubuwan Dake Karawa Hakora Haske

Lura da hakori na daya daga cikin hanyoyin dakan kara fitar da kima hadida kamalar mutum. Duk yadda mutum yakai ga iya kwalliya hadida kwarewa wurin daukar wanka daxarar yagaxa tafannin kula da hakoransa saikaga gabadaya kwalliyar ta lalace, dankuwa yagaxa tafannin bawa hakoransa kulawar data dace. Danhaka wannan wata hanyace daxata dawowa mutum kima, martaba hadida darajar hakoranki/ka koda kuwa hakoran sunyi irin baki ko tsatsa tacikine haka kuma yakan yaki kwayoyin cutar dakan haifarwa mutum warin baki.

 1-STRAWBERRIES:Kinemi ganyen itacen strawberry kiyankashi kanana- kanana kidinga cuda hakoran dashi, yana sanya hakora haske sosai haka kuma yana kore dattin dake makalewa ajikin hakora, hakanan yana sanya baki fitar da iska me dadin kamshi. 

2-LEMON ZAKI(Orange): Kisamu lemon xaki mekyau meruwa kiyanka kimatse ruwan sannan ki guntsi ruwan abakinki sannan kisanya brush kidinga diddirxawa lungu da sako sannan kixubar kiwanke da ruwa. Yanasa hakora suyi kashar kamar kankara. 3-LEMON TSAMI(LEMON) Kisamu lemon tsami kiyanka ki matse ruwan sannan ki sanya abakinki kiwanke kowane lumgu da saki na bakin, yana fitar da duk wani dabbara- dabbara dakan makale a hakori.

 

 
SIRRIN FARAREN HAKORA
 

Yawancin mutane ba su da masaniyar yadda zasu magance matsalar rashin fararen hakora wasu har suna zaton halitta ne, to ga hanya mai sauki Kamar yadda kowane sashi na jikin dan Adam yake bukatar kulawa, haka zalika Hakora ma na bukatar kulawar mai su. hanyoyin da za’a bi cikin sauki don samun lafiyayyun hakora masu haske da sheiki har ma su rika walkiya. Hanyoyi sune kamar haka:

Dabi’ar cin abinci Da farko dai sun bayyana cewa dole mutum ya canja dabi’arsa ta cin abinci, ma’ana mutum ya kasance yana cin abubuwa mai gina jiki, kuma yana da kyau ya gujewa cin abincin da yake da tarin sukari a cikinsa (Sugar). Ta’ammali da abubuwan da suka da hada Madara, Nono da kuma shan wadaccen ruwa mai tsafta da sauransu yana inganta lafiyar Hakori

Amfani da Danko (Chewing Gum): Taunar Danko wato wanda aka fi sani da Chewing gum a turance yana taimakawa matuka gaya wajen hana zaman wani abu a cikin sakon hakori, a sanadaiyyar hakan ka iya jawo tsutsar hakori dama sauran dangogin matsalolin da suka shafi hakorin baki daya. Amfani tare da

sauya magogin baki (Toothbrush): Yana da matukar muhimmanci, wanke baki akai-akai domin yin hakan zai taimaka wajen wanke tare da fitar da duk wani nau’in abun da ya makale a hakorin. Haka zalika yana da kyau ace mutum yana sauya magogin bakinsa duk tsawon wani lokaci (a kalla duk bayan wata uku). Bayan amfani da magogin baki yana da kyau ace an wanke da ruwa mai tsafta sannan a barsa ya bushe tare da samar masa wajen ajiya mai kyau, amma kar ya zama ana barinsa a bayan gida (Toilet) kamar yadda wasu suka maida dabi’arsu, wanda hakan ka iya jawo wasu kwayoyin cututtuka su hau kan shi magogin bakin. Hanyoyi 8 da za ku bi domin Association, ta bayyana cewa kaso 42% ne na mutane ke amfani da magogin baki domin kula da lafiyar hakori. Sun sake jero wasu hanyoyin da suke ganin yin su zai taimaka gaya wajen samuwar ingantattun hakora; Wanke baki da magogi har na tsawon mintuna biyu (2 Minutes) akalla sau biyu a rana. Kuskure baki da ruwa lokaci zuwa lokaci, musamman bayan kamala cin abinci ko wani abu mai dauke da abun da zai iya zama a hakori. Amfani da maganin wanke baki wanda da dama daga cikinsu suna dauke da sinadarin kariya (Antibacterial) wanda yana taimakawa wajen wanke duk wani abu tare da karawa hakora kwari.

Ganin Likitan Hakori: ziyara ga likitan Hakori yana da matukar amfani, saboda yin hakan zai taimaka wajen duba da irin halin da hakoran ke ciki, sannan in har akwai wani abu da yake damun hakoran, likitan zai iya bada shawara ko magani domin kauda cutar tun kafin ta zama babba. Likitan zai iya yin wankin Hakori wanda hakan zai bawa mai su damar jin dadi sosai, kuma yana da kyau ake yin wanki hakori akalla sau daya a shekara. 

 Karin amfani da sinadarin Vitamin: Kamar yadda bayanai suka gabata cewa, a kaucewa cin abubuwa masu sukari da yawa, a nan kuma an bayyana cewa amfani da abinda yake dauke da sinadarin Vitamin zai taimaka sosai. Cin abinci mai dauke da ganyayyaki kamar su kabeji, Salak, lansir,Zogale da sauran Ganye yana da amfani. Cin kayan itatuwa kamar lemo, Ayaba, Kankana, Inibi duk suna da fa’ida sosai wajen lafiyar hakori. Har wayau, cin abinda ya shafi nau’in abinda ke cikin ruwa kamar su Kifi, da sauransu wanda duk suna dauke da nau’in Vitamin D zasu taimaka gaya.

Amfani da Man Kwakwa: Mutum zai iya amfani man kwakwa wajen wanke baki. Cokali daya na man kwakwa mutum zai diba ya wanke bakinsa har na tsawon mintuna 20 har sai yawun bakin mutum da man kwakwar sun canja launi zuwa launin madara, sannan a zubar amma fa kar a hadiye.

Mutum zai iya hada man wanke baki da kansa Makilin (toothpaste) i Akwai abubuwa da akan yi amfani da su domin hada abun wanke baki, wannan abubuwa su ne kamar haka:

Cokali 4 na hodar Calcium
Cokali 1 na Stevia Cokali 1 na Gishiri (salt)
Cokali 2 na Baking Soda
Kaso ¼ na kofin man kwakwa
Wadannan su ne jerin hanyoyin da in kunyi amfani da su zasu taimaka wajen kara tsaftar hakori tare da kara musu inganci. 

 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top