Babu shakka masana sun yi itifakin cewa rashin gamsuwa a wurin saduwar iyali a tsakanin ma'aurata na daya daga cikin manyan dalilai dake haddasa matsaloli da a wani sa'ilin take janyo mutuwar aure.

Binciken masana kiwon lafiya da kuma kwararru a kan nazarin abinci da ake kira da nutritionist a harshen turanci, sun haskaka cewa ci abinci mai kyau da motsa jiki da kuma yawaita tunani mai kyau na iya inganta lafiyar da ni'imar ma'aurata.

Tabbas nau'o'in abinci wadanda ke dauke da sunadarai masu sanya farin ciki ga mutane sun kunshi wasu abubuwan gina jiki masu alaka da gamsuwa da kuma bunkasar ni'ima a yayin jima'i.

Musamman sunadarin zinc dake taimakawa wajen magance matsalolin haihuwa tsakanin maza da kuma kara yawan maniyyim da namijin ke samarwa. Nau'in abinci masu dauke da sunadarin zinc sun hadar da jan nama, naman ruwa masu kwanso da kuma dangin 'ya'yan kabewa, na gyada da kuma madara.

A cewar masana soyayya, cin cakulet mai duhu zai iya kara bunkasa ni'imar ma'aurata a sakamakon sunadarin phenylethylamine (PEA).



Sunadarin trytophan dake samuwa cikin nau'in abinci irin su kifi, kwai, gyada, alayyahu, kaji, waken suya da kuma 'ya'yan itace, sun kan taka muhimmiyar rawar gani wajen kar dankon soyayya a tsakanin ma'aurata.

Hakazalika dafaffen attaruhu mai dauke da sunadarin capsaicin, ya kan taimaka wajen kara yawan zafin jiki da kuma bugawar zuciya cikin sauri tamkar yadda yake ta'allaka a yayin saduwa da iyali.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top