Daga Ibrahim Baba Suleiman
Sheikh Isa Ali Pantami PhD na ɗaya daga cikin aminan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta fannin aiki da gaskiya da riƙon amana. Kazalika bai tsaya iya nan ba, a duk wani abu da ya taso yakan keɓe da shugaba Buhari ya faɗa masa gaskiya, kuma shugaban ya yi amfani da shawarar Pantami sannan ya ɗauki mataki nan take, tunda ya samu damar da duk lokacin da yaso yaga shugaban ƙasa zai ganshi.
Wannan ba ƙaramar Nasara bace ga duk wani Musulmi Ahlussunnah a faɗin ƙasar nan, wanda a baya sai dai kaga masu ƙarancin ilimin addini ne ke jagorantar Al'umma, basu ganin darajar addinin kansa, bare Malaman addinin.
Dr. Pantami a lokacin da ya jagoranci Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta zamani ta Najeriya (NITDA), yayi namijin ƙoƙari wajen jajircewa akan aikin, wanda kafin zuwansa ire iren mu bamu ma san da hukumar ba kwata kwata, amma zuwan Pantami sai da ya zaƙulo aikin kowa yasan aikin, kuma aikin ya taɓa ɓangarori daban daban a sassan ƙasar nan.
A wannan mataki na gaba cikin muradin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ire-iren su Dr. Isa Ali Pantami ma'aikata, ina ka fito aiki, ina zaka aiki, ya dace a zaƙulo domin su rufa masa baya wajen ganin an cikawa ƴan Naijeriya Alƙawarin su, Musamman yankin mu na arewacin ƙasar waɗanda yankunan kudu suka mana fintinkau a fannoni daban daban na ci gaba
Zaɓin Dr. Isa Ali a matsayin ministan ƙasa, akhairi ne a jiharsa ta Gombe, ganin yadda ƴan siyasar jihar kowa yaja daga ana ta kace nace, sai Allah ya turo Raba gardama "Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami Phd".
A ƙarshe ina mai rufe rubutuna da shawarwari ga sabon minista, na a ɗan ƙara buɗe ƙofa ga ƴan siyasa, Malamai, matasa tare da dattawa wajen ganin an samar musu abunyi ta fannin aikin gwamnati, kananan kwangiloli da manya ga ƴan ƙasa da jihar da ka fito kamar yadda ka saba a baya.
Ina addu'ar Allah ya maka jagora, ya baka ikon sauke nauyin da Allah ya ɗora maka, yasa a baka wajen da zaka iya tallafawa ƴan ƙasa. Amin
©HausaLoaded
Post a Comment