Yayinda shugaba Muhammadu Buhari ya aika sunayen ministocin da yake niyyar aiki da su a wa'adinsa na biyu, an samu sunan babban shehin Malamin addini, Sheik Dakta Isa Ibrahim Ali Fantami, matsayin minista daga jihar Gombe.

Sheik Isa Ali Fantami a yanzu haka yana rike da kujerar shugabancin hukumar cigaban ilimin komfuta na zamani wato NITDA.

Wannan abu ya farantawa yan Najeriya musamman yan arewa wadanda suka san Sheik Isa Fantami.

Duk da kujerar gwamnati da yake rike da shi, Sheik Ali Fantami bai daina gudanar da karatu da wa'azi ba. Har ila yau yana gudanar da tafsirin watan Ramadana a masallacin Annur dage unguwar Wuse 2 Abuja.

Hakazalika kowace ranar Lahadi yana karantar da al'umma littafan Shama'ilun Nabiy a masallacin Wuse Annur.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top