![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgq0Xg95jAxs1Evdxe6YQSm3HB2gsgcqlxQy2NF8b0W69zjSKK3jC7-MXL574fUD_XorStBlHiNidEC9vgTi0Qe7lTdkMeqC-Y2NN3V5lJy8CMCnGn3_HY_-ASQ4HI80W3z9Y141ZcDJEgY/s1600/2019-07-25--21_11_26.jpg)
A yayin da majalisar dattijai ke tantance daya daga cikin sanatocin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya aika musu, Ramatu Tijani Aliyu, shugaban marasa rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe ya bukaci a barta ta wuce ba tare da tambaya ba.
Shugaban majalisar, Yahaya Abdullahi da yake goyon bayan maganar shugaban marasa rinjaye ya bayyana Ramatu a matsayin me jajircewa wajan aiki wanda a turanci ya bayyanata da "Dutifu Lady" kawai sai 'yan majalisar suka fashe da dariya inda a tsammaninsu kalmar "Beautiful" yayi amfani da ita dake nufin kyakkyawa.
Saida aka kwashe kusan minti 5 Abdullahi nata maimaita "Dutiful" dan ya wanke kanshi sannan daga baya aka samu nutsuwa a majalisar.
Sanata Aliyu Sabi Abdullahi daga jihar Naija, ya tashi inda ya kare sanata Abdullahi yace sauran sanatocin basu mai adalciba dan kuwa sun mai mummunar fahimta.
Post a Comment