Gaskiya a yanzu alhamdulillah, tunda babu inda yake yi min ciwo a jikina tun daga lokacin da aka yanke wannan kafa. Kuma akwai wata allura da aka yi min a baya saboda kashe kaifin ‘kafafuwan wadda ita ce ke dan damuna a yanzu. Amma a jikina a yanzu babu wata matsala da nake ji. Na kuma yi wa Allah godiya bisa yanke wannan kafa da aka yi wadda ita ce babbar lalurata.
Tsawon wata nawa ka yi da wannan ciwo?
Ai yanzu ina kusan shekara 12 ke nan ina fama da wannan jiki amma daga shekarar 2003 ne zuwa yanzu da muke magana aka samu tsanantar rashin lafiyar. Kamar yadda ka sani ne a bara na kwanta a wannan asibiti na Barau Dikko inda aka cire min ’yan yatsu. A lokacin har an yi yajin aiki amma Shugaban Asibitin ya dage ya nemi kada a je wancan yajin aiki wanda a lokacin ne aka cire min yatsu biyu kuma a wancan lokaci shi da kansa Alhaji Musa ne ya yi min wannan aiki. A wancan lokaci na samu sauki ina zuwa aiki ina zuwa wajen harkokina har ina tuka mota. Amma daga bisani ciwon ya dawo inda aka mayar da ni kafin a sallame ni in koma gida.
Kwanaki kusan bakwai ke nan da aka dawo da ni asibitin wato ranar Alhamis waccan da ta wuce aka yi min aiki.
Wace cuta ke damunka?
Ciwon suga ke damuna yakan hana ni yin barci domin a lokacin awon cutar sukarin kan kai har 20 da ’yan digo; amma a yanzu bai wuce shida zuwa bakwai.
Sai ga yadda Allah Ya kaddara a kanka har an yanke maka kafa me ka ji?
Na fi kowa murna saboda jarrabawa ce daga Ubangiji babu wanda ya saka min. Kuma babu wanda ya isa ya cire min sai Ubangiji. Kuma daga cikin rukunan imani akwai cewa mutum ya yi imani da kaddara ta sharri ko khairan.
To, abin da na sani a rayuwa ta duniya shi ne wannan wata lalura ce daga Allah Wanda Shi Ya dora min kuma ban zargi kowa ba.
A ranar da aka dawo da ni asibiti sai suka ce abin da ya fi dacewa shi ne a yanke kafar, sai na fi kowa murna kamar ranar da aka ba ni takardar zuwa Aikin Hajji. Na ji dadi da farin ciki domin ni na san halin da nake ciki. Kuma wata hanya ce har ila yau da Allah Ya kawo min don samun waraka. A da ba na iya cin abinci ba na kuma iya yin magana ballantana kuma in biya wa kaina bukatar zuwa bayi dole sai an dauke ni.
Amma a yanzu an wucen wurin. Ina kuma yin amfani da wannan dama domin yin godiya ga Allah da Ya kara ba ni lafiya.
Ko ka samu taimako daga gwamnati ko al’ummar gari?
Hakika na samu daga mutane daya bayan daya masu zuwa duba ni. Wadansu kuma suna bukatar lambar asusun ajiyata su turo min kudi. Haka kuma Kungiyar ’Yan Wasan Kwaikwayo (Fim) ta Kano da Shugaban ’Yan Wasan Fim ta Kasa Abdullahi Maikano da na Jihar Kaduna duk sun kawo min ziyara domin ganin halin da nake ciki. An kuma hada abubuwa an kawo min
Idan Allah Ya ba ka lafiya ko za ka ci gaba da wasan kwaikwayo?
Wannan ai ba zai hana ni ci gaba da sana’ata ba. Bayan haka kuma ai ni ma’aikacin gwamnati ne na kuma gode wa Allah da na yi nisa a aikin gwamnati domin har na kai matakin albashi na 13. Saboda haka wannan ba zai hana ni ci gaba da sana’a ba domin kashi 90 na jama’a sun san ni ne a sana’ar wasan kwaikwayo ba su san ni a matsayin ma’aikacin gwamnati ba.
Wannan wata dama ce da zan ci gaba da yin sana’ata ba tare da na sa wa kaina wani tunani ko tsamgwama ba. Wadansu ai za ka gan su jiki suke ja, wadansu kuma kafa wadansu kuma yatsu ne ba su da shi sai baki amma kuma suna rayuwansu kamar kowa. Kamar yadda na ce maka ne Wanda Ya dora min wannan lalura Shi ne zai cire min kuma Shi ne zai ba ni harkokin rayuwa har zuwa lokacin da zan koma gare Shi har zuwa Ranar Tashin Alkiyama.
Mene ne sakonka ga masoya?
Ba ma ga masoyana kadai ba ga duk wadanda ke ra’ayina da wadanda ba sa ra’ayina, ina godiya ga kowa da kowa musaman a kan addu’o’in da suka rika yi min. Domin wani ba ya da ko taro da zai ba ka; amma yana yi maka addu’a kuma addu’oi’n sun taimaka ana samun biyan bukata. Kamar yadda na fada maka ni a ranar da za a yi aikin ji na yi kamar a ranar zan tafi Aikin Hajji.
Da zan shiga dakin aikin sai na rika daga wa iyali da yara hannu. Da muka shiga ciki ina kuma jin yadda ake satar kashin kafata abin da kawai nasa a gaba shi ne addu’o’i. Saboda haka na ga falalar addu’o’in da jama’a suka rika yi min tare da fatar Allah Ya sa su yi sanadin shigarmu Aljanna baki dayanmu.
Ina kuma yin amfani da wannan dama in yi kira ga jama’a cewa ni ban bai wa kowa wani lambar asusun banki da sunan a nema min taimako ba. Don haka duk wanda zai aika kudinsa idan bai ga an rubuta Sani Idris Kauru ba to ba asusuna ba ne. Kuma masu yin amfani da sunana domin yin cuta su bari don Allah domin hakan bai dace ba, na gode.
® Aminiyahausa
©HausaLoaded
Post a Comment