Mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, ya dalilin da sanya gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ki bin umurnin kotun da Alkali Gabriel Kolawale ya bada na sakin shugaban kungiyar mabiya akidar Shi'a, Sheik Ibrahim Zakzaky.

Adesina ya laburta a hirar da yayi da tashar Channels TV ranar Lahadi cewa dalilin kawai shine gwamnati ta daukaka karar Shari'ar.

Kakakin shugaban kasan yace tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami ya san hikimar da ya sanya gwamnati ta daukaka karar.

Yace: "Na san tsohon ministan shari'a ke da hurumin magana akan wannan lamari. Idan an bada beli kuma aka daukaka kara, wajibi ne a jira a yanke hukunci."

Saboda haka wannan lamarin kotu ne kuma ya fita da hurumin na. Kamar yadda muka sani idan ba'a kammala shari'a ba, babu wanda zai iya cewa an kammala."

Adesina ya ce ana gurfanar da El-Zakzaky a kotun Kaduna kuma ranar Litinin za'a sake sauraron belin da ya nema.

Saboda haka ya yi kira ga yan Shi'a su jira kotu ta yanke hukunci.

Yayinda yake amsa tambaya kan yadda yan sanda suka harbi yan Shi'a ranar Litinin, Adesina ya ce ai kamata yayi a yabawa yan sanda saboda irin nuna kamewa da suka yi; saboda da sun nuna karfinsu, da mutuwan ya fi haka yawa.

®Fb) Nijeriyarmu a yau

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top