![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEg-VzTlw1Zbt7bJkQOdYDqSZ1lpSj9vrWYwNpE1vdarNlVEsBk7AwevC6de_APSEvGZiTz0NxMSUpq4drKHTfh_emoE4Txj8mHPWWekHpK7vzC29QjqiCJB6rR3fslytmW6ALiEW_xUC2YY/s1600/ic-9612.jpg)
Tun kamin fito da sunayen sabbin ministocin shugaban kasa, Muhammadu Buhari labarai ke yawo cewa za'a baiwa tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu, Ministan wasanni, bayan fitowar sunayen a Jiya, Talata, wasu taurarin Kannywood sun fara kiran cewa ya kamata a baiwa Alin mukamin minista.
Ali Artwork na daya daga cikin wanda suka fara wannan kura inda ya rubuta a shafinshi na Instagram cewa, ko suna so ko basa so muna nan akan bakanmu na cewa sai an baiwa Ali Nuhu ministan wasanni.
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhBu5P5DLq9cOt3Cgbw4ikV5T0pKRE39GznHqybpG3qcT4Cz7vheC_GhoHcHvKomW9SSvllAZuMTccBX3W8g8PvGTVlBTUQSJDVhMcetl_Bg-nguQscVpU-r7lwxHs__l8lI3G-xGTMx-km/s1600/ic-4239.jpg)
Hakanan shima Abbas Sadiq yayi kiran cewa ya kamata a baiwa Ali Nuhun ministan wasanni dan ya cancanta.
![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEincbGYRmEVDzrtB2vfFq-2cOVtBVAabKf2DWLtFKlIWZpokPZwhyphenhyphen_fhX08AuZXU2hhcYGjK8hMWjo07eYnIsRPJBbzUtoQyPyoyqTyj_9YcKMBtFbZNenY5F95gg1w0lv9uXBWPFzFJ_9d/s1600/ic-452.jpg)
Taurarin masana'antar Kannywood sun bayar da gudummuwa sosai kisan za'a iya cewa fiye da ta kowane lokaci a baya a babban zaben 2019 wanda shugaba Buhari ya samu nasara.
Post a Comment