A yanzu haka, wani sashen ma'aikatar hukumar bada agaji na gaggawa ta kasa wato NEMA dake Abuja na ci bal-bal.

Hakazalika an bankawa motocin hukumar biyu wuta kuma jami'an kwana-kwana na cikin kashe wutan yanzu.

A cewar The Cable, Wani mai idon shaida ya bayyanawa manema labarai cewa yan kungiyar Shi'a mabiya Sheik Ibrahim El-Zakzaky da suke gudanar da zanga-zanga suka bankawa ma'aikatar wuta lokacin da yan sanda suka hanasu zanga-zanga.

Zanga-zangar wacce suka fara daga tashan NITEL Junction dake Wuse 2 ya samu cikas ne yayinda yan sanda suka toshe hanyar zuwa majalisar dokokin tarayya da fadar shugaba kasa

Kawai sai yan sanda suka fara harbe-harbe yayinda yan Shi'an ke kokarin shiga farfajiyar Eagle Square. Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu kawo yanzu.

Wani dan Shi'a yace: "Za mu cigaba da zanga-zanga, kuma idan basu son ganinmu a kan titi, gwamnati ta saki shugabanmu. Idan suna son kashe, su cigaba da kashemu."
Gawar da anka kashe


Ga bidiyo



©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top