Yarjejeniyar na daga cikin tattaunawa da shugaban kasa Buhari ya yi da shugabar kasar Jamus Angela Michael a wata ziyara da ta kawo Najeriya a watan Agustan 2018.

Bikin rattaba hannun da ya gudana a zauren majalisar zartaswar tarayya da ke Aso Rock Villa. Bisa yarjejwniyar, Nijeriya ta yarda da hadin gwiwar ne domin samar da Mega Watt dubu Bakwai (7,000) na karfin makamashin hasken wutan lantarkin daga nan zuwa shekarar 2021, sannan da karin Mega Watt dubu sha daya (11,000) zuwa shekarar 2023 wanda zai ba da jimillar Megawat dubu 25,000 na karfin wutan na kasa baki daya.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top