Daga Rilwanu Labashu Yayari

Tsohon mininstan na kasashen waje a lokacin mulkin Jonathan ya ce "Kamar yadda mu ka saba duk ranar Juma'at, yau ma ni da Baba mun yi tattakin kilomita takwas (8) zuwa masallacin Dr Ali Isa Pantami na Annoor da ke Wuse a Abuja. Dr Pantami na d'aya daga cikin malaman da na ke gamsuwa da wa'azinsu.

Sai dai a yau abun da ya fi jan hankalina shine addu'a da aka gabatarwa Malam a cikin hud'uba ta Allah ya tallafi hannunsa a kan wannan aiki na Minista da zai fara nan ba da dad'ewa ba.

"Hakan ya sa na tuna da cewa shekaru takwas da su ka wuce, ni kaina na samu kaina a cikin irin wannan yanayin. Duk da ya ke cewa a lokacin ni shekaru na 33 ne kawai, kuma ban ta6a rik'e wata ma'aikata ba, idan ka kwatantani da Mallam da ya ke shekara 47 ga kuma babbar ma'aikata da ya ke rik'e da ita a yanzu, amma babu abun da Dr Pantami ke buk'ata face addu'ar samun nasara.

Domin ba kowane zai shiga wannan aiki na Minista ba, ya kuma iya yin aikin da har za'a yaba ba, bai kuma bar abun kunya ba sai wadda Allah (SWT) kawai ya kare".

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top