Man-zaitun ( Olive oil/ Olea europea ) wani irin nau'in mai ne da ake samarwa daga 'ya'yan itaciyar zaitun (Olive tree). Ana amfani dashi wajen girki, gyaran fata, magani, hada sabullai da kuma man-fitila ( a gargajiyance). Man-zaitun ana amfani dashi a 'kasashen duniya da dama, musamman kasar Spain, France (Faransa), Italy, Greece (kasar Girka), Syria, Lebanon, Egypt, Libya,Tunisia, Algeria, Morocco da sauransu. Toh amma kasashen da suka fi yawan amfani dashi sune Portugal, Spain, Italy da Greece. Daga shekara ta 2000 zuwa ta 2009, kasashe 3 da suka fi yawan samar dashi sune: 1. Spain 2. Italy 3. Greece. Kasar Syria itace ta 4 , sai mai-bimata kasar Tunisia, a matsayin ta 5. Sabili da muhimmancin itaciyar zaitun, Allah Madaukakin sarki, Mai -halittu ya ambace ta a cikin Al-Qur'ani Maigirma - Surat At- Tin da Surat An- Nur. Man-zaitun nada amfanin sosai ga lafiyar 'dan adam. Binciken ilimin kimiyya ya nuna cewa yana da amfani kamar haka: 1. Yana 'karfafa garkuwar jiki ( domin yaki da kwayar cutar biras, bacteriya, fangas (fighting virus, bacteria, fungus etc.) da sauransu. Wadannan cututtuka suke haddasa matsalolin lafiya da dama, kamar irinsu ciwon-anta, tetanus da cin-ruwa. 2. Yana da sinadarai masu bada kariya daga kamuwa da ciwon daji (rich in antioxidant subtances). 3. Kariya daga cututtukan zuciya - yana rage yawan sinadarin kolestirol (reducing high cholesterol) wanda idan yayi yawa a cikin jini yake da illa ga zuciya. 4. Rage hawan jini (reducing high blood pressure). 5. Taimako ga masu ciwon-suga (helping diabetic patients). 6. Kariya daga ciwon jiki (sanyin jiki) dana gabobi (anti-rheumatism & arthritis). 7. Inganta lafiyar zuciya (improving heart's function esp. to older people whose hearts are weak due to aging) musamman ga tsofaffi wanda zuciyar su ta fara rauni wajen aiki saboda tsufa. Yana gyara zuciya da quruciya. 8. Kariya daga ciwon daji dake shagar fata ( protection from skin cancer). 9. Inganta lafiyar qashi. (improving bone health). 10. Inganta lafiyar kwakwalwa wajen koyon wani abu kamar karatu ko rike karatun, musamman ga manya (improving cognitive function) da sauransu. Ana iya amfani da man-zaitun kamar haka: ~ Asha cikin babban cokali sau 2 a rana - safe da rana, cokali daya a kowane lokacin. ~ Ayi girki dashi a matsayin man girki ko a zuba cikin abinci bayan girki. ~ Manshafawa kamar sauran man amfani na jiki. ~ Giris ga ma'aurata (sex lubricant). Bugu da kari, zai kuma bada kariya daga cututtuka. ~ Ciwon-kunne, digo 2 ko 3 na man a cikin kunne. ~ Da sauran wasu hanyoyin na inganta lafiya.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top