Kofural Bashir Umar ya ce Muna dawowa daga sintiri, da yamma Na ga ambulaf a gefe hanya, daga nan na dauko shi, Ina tare da wasu mutane, amma na ki sanar dasu abinda ke cikin ambulaf din Na ga lambar waya a ciki don haka lokacin da muka dawo bakin shingen aikin mu, na kira shi. Wani mutum ya amsa, sai na ce masa mun sami wani kunshi, sai ya amsa da cewa ambulaf mai ruwan kasa, wanda aka sanya sunan Alhaji Ahmed!' na ce dashi Eh, yazo daidai Rukunin Sojan Sama yasameni. Mutumin ya zo, yayi parking a motarsa ​​a waje, kuma na tafi don haduwa da shi. Sai na ba shi kunshin, sai ya gaya mini abin da ke ciki, € 37,000, wanda ya kirga kuma ya tabbatar sun cika. Ya yi godiya matuka, ya tambaye ni wane lada nake so daga gare shi, saboda na taimaka masa sosai, ya kara da cewa mutane da yawa ba za su mayar da kudin ba. Na ce masa bana bukatar komai daga gare shi, saboda aikina yana biya min dukkan bukatuna, Na ce masa Allah yasa bazakai asarar dukiyarka ba, na same shi, kuma yanzu na mayar maka su, Don haka, ya tafi. Daga baya, muna tattaunawa da abokin aikina Abubakar, wanda shi ma abokina ne, kamar yadda ya ji ni na yi magana da mai kudin a waya, da kuma yadda na ce ya kamata yazo karbe su. Abubakar ne ya fara gaya wa mutane;

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top