Premium Times

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kammala shiri tsaf don bayyana ƙungiyar IMN, Shi’a a matsayin haramtacciyar ƙungiya a ƙasarnan.

Hakan ya biyo bayan bayanan kud-da-kud ne da PREMIUM TIMES ta jiyo daga majiya masu ƙarfi.

Ana sa ran Buhari zai bayyana wannan shiri na gwamnati ne ko a cikin daren yau ko kuma zuwa gobe Talata.

Babban dalilin da ya sa Buhari zai tabbatar da haka kuwa shine ganin irin yadda ƴan shi’a suka canja salon zanga-zangar, ya koma hare-hare da arangama da suke yi da ƴan sanda da har sai anyi jina-jina a duk lokacin da suka fito.

Buhari ya tausaya wa ƴan sanda ganin cewa abin na neman yafi ƙarfinsu kuma ba za a iya tura sojoji ba domin abin bai kai a shigo da su ba.

Tun bayan arangamar da ƴan sandan suka yi da ƴan shi’a masu zanga-zanga shugaba Buhari ya shiga ganawar gaggawa da jami’an tsaro domin sanin abinda za a yi a kai cikin gaggawa.

Arangamar ƴan sandan da masu zanga-zanga, ƴan Shi’a yayi sanadiyyar rayukan mataimakin kwamishinan ƴan sanda Usman Umar da kuma wani matashi mai aikin bautan ƙasa dake tare da gidan talabijin din Channels.

Sannan su kan su ƴan shi’an sun bayyana cewa sun rasa mabiya shida a wannan artabu da akayi da ƴan sanda.

Gidan talabijin ɗinne ta sanar da haka a labarun dare inda tace duk da an garzaya da matashin asibiti cikin gaggawa, ashe lokaci yayi, ya cika.

Idan Buhari ya saka hannu a wannan doka, wannan ƙungiya ya zama haramtacce kenan a kasar nan.

Dama can Buhari ya bayyana ƙungiyar IPOB a matsayin haramtaccen ƙungiya sai kuma gashi yanzu idan har an tabbatar da hakan, ƙungiyar IMN zai zama na biyu kema.

Me za Ku ce kan haka?

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top