- Jarumin ya bayyana cewa yanzu harkar fim madubi ce kawai ga mata wadanda suke so a haskasu duniya ta san su
- Ya bayyana cewa yanzu babu wani abu da matan ke yi idan ba bin mazan banza masu kudi ba da kuma masu mulki
A wani rahoto da muka samu a shafin jaridar Hausa Trust ya bayyana yadda shahararren jarumin wasan Hausan nan na masana'antar Kannywood, Alhaji Tanimu Akawu, wanda ya bayyana cewa yanzu haka ya kai kimanin shekaru goma sha takwas yana fafatawa a harkar fim.
A wata tattaunawa da aka yi dashi a wani gidan rediyo mai suna Human Right dake garin Abuja, cikin shirin dandalin fina-finai, jarumin ya bayyana cewa matan fim din suna bin mazan banza masu kudi da masu mulki.
Jarumin ya bayyana cewa motar da Hadiza Gabon ke hawa kadai za ta iya siyan motocinsa guda goma, ya kara da cewa shi EOD ce yake hawa kuma ya siye ta da kudinshi.
Ya cigaba da cewa, "Fim yanzu madubi ne na mata, duk macen da kaji tace za ta yi harkar fim, tana so a haskata ne kawai ta samu kudi."
Jarumin ya kara bayar da misali da jaruma Maryam Yahaya, ya ce, "Kallo kawai ta zo yi aka sanyata a cikin fim din Mansoor, amma yanzu wayoyin dake hannunta sun kai na kimanin dubu dari takwas, kasan kuwa ba a fim ta samu wannan kudin ba, saboda nawa ne duka ake biya a fim din?"
Ya cigaba da cewa, "Ko ni yanzu ka bani 'yar fim na aura bazan aure ta ba, saboda na san abinda ke tafiya a harkar, yarinya tun ba ta da wayo take kallon mu muna yin fim amma yanzu ta zo cikin shekara daya ta samu kudin da bamu taba tunanin zamu samu ba, yaya za ayi ta dinga ganin girman mu."
Mai gabatar da shirin Sabitu Garba Mustapha yayi mishi nuni da cewa wannan magana da yake yi babbar magana ce, inda ya bayyana mishi ya kamata ya tabbatar da abinda yake fada, sai jarumin ya bayyana cewa ai wannan abu kowa ya riga ya sani.
Majiyarmu ta samu wannan labari ne daga jaridar legit
©HausaLoaded
Post a Comment